Sauya sheƙa: APC ta maida gwamnonin PDP guda takwas

Spread the love

*Gwamnonin Zamfara da Taraba suna sansanar APC

*Yadda matsalar PDP ta samo asali, inji Fayose

*Waɗanda suka soke ni kan aiki da gwamnatin APC sun bi sahuna – Wike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Daga dukkan alamu dai babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya ta ɗauko hanyar tsagwanyewa gadan-gadan bayan da rahotanni suka nuna cewa, gwamnonin jihohin Zamfara, Dauda Lawal, da Taraba Agbu Kefas, suna duba yiwuwar koma wa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa, shirye-shirye sun yi nisa tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari da gwamnan jihar mai ci wajen ganin an amshi gwamnan a APC cikin watan Nuwamba mai kamawa, yayin da shi ma Gwamna Kefas na Taraba ake sa ran a kowane lokaci daga mako mai zuwa zai iya tsunduma cikin APC ɗin.

A baya-bayan nan, Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP bisa abin da ya kira “dalilai bayyanannu.” Matakin Diri ya kawo ƙarshen jita-jita da tsammanin sauya sheƙa da ke yaɗuwa a cikin harkokin siyasa, sa’o’i 24 kacal bayan sauya sheƙa da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, daga PDP zuwa APC. Haka kuma, akwai alamun cewa, Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, na iya barin jam’iyyar adawa ta PDP, duk da cewa ba a samu tabbacin hakan daga masu taimakonsa ba.

Da wannan sauya sheƙa, PDP ta ragu sosai, inda yanzu ke da gwamnonin takwas kacal, idan aka kwatanta da 12 da aka zaɓa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar a zaɓukan da aka gudanar a baya.

A halin yanzu, gwamnonin PDP su ne: Ahmadu Fintiri (Adamawa), Bala Mohammed (Bauchi), Caleb Mutfwang (Filato), Agbu Kefas (Taraba), Dauda Dare Lawal (Zamfara), Seyi Makinde (Oyo), Siminalayi Fubara (Ribas) da Ademola Adeleke (Osun). Kafin sauyar sheƙar Diri, Gwamnonin Sheriff Oborevwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom) da Mbah (Enugu) sun riga sun bar jam’iyyar zuwa APC.

Masana siyasa sun sha bayyana cewa, PDP na fama da matsaloli iri-iri, wanda hakan ke haifar mata da koma baya.

Diri ya bayyana sauya sheƙarsa a wajen taron faɗaɗa Majalisar Zartarwa na Jiha a Gidan Gwamnati, Yenagoa, inda ya ce ya yi haka ne bisa dalilai bayyanannu. A wurin taron, akwai Shugaban Majalisar Jiha, Abraham Ingobere, mataimakinsa Michael Ogbere, shugaba mai rinjaye na APGA, Edward Brigidi, da wasu ‘yan majalisa guda bakwai.

A cewar Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Daniel Alabrah, Diri ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin jihar. Ya yi godiya ga magoya bayansa da suka tsaya masa, yana mai cewa su ci gaba da goyon bayansa yayin da yake gina Bayelsa mai ƙarfi da tasiri.

Haka nan, tsohon zan majalisar tarayya daga Bayelsa, Senator Ben Murray-Bruce, ya sanar da murabus ɗinsa daga PDP. A cikin wani bayani da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa, “A karon farko a tarihin ƙasarmu, muna da Shugaba wanda ya fahimci harkar kuɗi da gaske, wanda ke kallon tattalin arziki ba a matsayin salon siyasa ba, amma a matsayin tsari mai rai da ya kamata a daidaita, a sassauta, kuma a bar shi ya numfasa.”

Tsohon ɗan majalisar ya ce ya san Shugaba Tinubu tun 1998, yana mai cewa: “Ba ya aiki ne saboda yabo, sai dai saboda sakamako. Kuma a yau zan iya tabbatar muku cewa yana kan hanya madaidaiciya.”

Game da yanayin sauya sheƙa, tsohon Gwamnan Bayelsa, Diri, ya zargi gwamnonin da suka koma APC da gujewa matsalolin da kansu suka haifar.

A ɓangarensa, Ministan FCT, Nyesom Wike, ya ce sauya sheƙa da ake yi na nuna cewa Tinubu na jagoranci mai hangen nesa da amfani. A wajen taron fara aikin manyan titinan Outer Southern Eɗpressway a Abuja, Wike ya ce, “Ina kallon talabijin da kafafen sada zumunta kullum. Mutanen da suka ce ina son tarwatsa PDP yanzu duk suna APC. Don haka, idan haka ne, su gode min saboda na shimfiɗa musu hanya.”

Haka nan, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, yayin naɗin kwamitin sadarwa na taron PDP, ya bayyana damuwa kan yawaitar sauya sheƙa, amma ya ce ana ƙoƙarin ci gaba da haɗa jam’iyyar kafin taron ƙasa na 15–16 ga watan Nuwamba a Ibadan.

Yadda matsalar PDP ta samo asali – Fayose

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba.

Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba.

A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita.

Ya ƙara da cewa, yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

“Ba daidai ba ne a zargi Tinubu saboda ficewar Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, zuwa APC,” inji Fayose.

“Su da kansu suka yanke shawara saboda PDP ta rasa shugabanci da tsari.”

Fayose, wanda ya mulki Ekiti sau biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar ta kasa koyon darasi daga kura-kurenta na baya, kuma ya sa ta zama mai rauni.

Ya kuma zargi wasu shugabannin PDP da yin siyasa don amfanin kansu maimakon ci gaban jam’iyyar gaba ɗaya.

Maganganunsa na zuwa nedaidai lokacin da ake cece-kuce a Nijeriya kan yiwuwar komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa ke ci gaba da komawa APC gabanin zaɓen 2027.

’Yan PDP da suka soke ni kan aiki da gwamnatin APC yanzu sun koma jam’iyyar – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sake rura wutar cece-kuce a siyasa, inda ya yi wa tsoffin abokan hamayyarsa dariya, yana cewa waɗanda suka taɓa sukar sa saboda aiki tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC, yanzu sun koma jam’iyyar da suka zarge shi da taimakawa.

Wike, wanda ya kasance jigo a jam’iyyar PDP, ya shiga gwamnatin APC tun bayan zaɓukan 2023, abin da ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyarsa ta asali.

Yayin bikin fara aikin gina babban titin Outer Southern Eɗpressway a Abuja, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya yi wa masu sukar sa kaca-kaca, yana kiran su “munafukai” saboda, a cewarsa, yanzu su ma sun bi sahun da suka taɓa zarginsa da ɗauka.

“Na kan ga a talabijin da kafafen sada zumunta, wasu na cewa ina lalata jam’iyyar, ina aiki wa APC. To yau, dukansu sun koma APC. Idan haka ne, ya kamata su yaba min saboda aikin da na yi musu,” inji Wike.

Wike ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ake ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo nasara ga Shugaba Tinubu a Ribas duk da kasancewarsa dan PDP.

Wannan mataki nasa ya zurfafa rabuwar kai a cikin jam’iyyar PDP, lamarin da daga baya ya kai ga ficewar wasu gwamnoni da jiga-jigai zuwa APC.

Wike ya jaddada cewa goyon bayansa ga Shugaba Tinubu ba ya da nasaba da son rai, illa kawai gaskiya da imanin da yake da shi kan shugabanci nagari. A cewarsa, ficewar waɗannan gwamnoni daga PDP ta tabbatar da daidaiton matsayinsa tun farko.

A ‘yan kwanakin nan, PDP ta sake fuskantar koma baya bayan jerin sauye-sauyen jam’iyya da suka faru a matakin gwamnoni.

A ranar Talata, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da komawarsa APC tare da kwamishinoninsa, shugabannin ƙananan hukumomi 17, da kashi 80 cikin 100 na shugabannin jam’iyyar PDP a jihar.

Bayan kwana ɗaya, Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri, shi ma ya sanar da barin PDP, yana mai cewa dalilinsa “a fili yake”, ko da yake bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba.

A cikin watanni shida da suka gabata, PDP ta rasa aƙalla gwamnoni huɗu zuwa APC — Sheriff Oborevwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom), Peter Mbah (Enugu), da Duoye Diri (Bayelsa).

Ga Wike, wannan ba kawai lamari ne na siyasa ba, illa hujjar cewa tarihi ya tabbatar da cewa shi ne ya tsaya kan gaskiya.

“Waɗanda suka ce na ci amanar PDP yanzu suna inda suka ce zan tafi. Idan wannan ne cin amana, to lallai na taimaka musu,” inji shi cikin murmushi.

Wike, wanda ke samun yabo saboda ayyukan gina tituna da sabbin gine-gine a Abuja, ya ce zai ci gaba da aiwatar da manufar “Sabon Fata” ta Shugaba Tinubu, yana mai cewa, “A siyasa, abin da ya fi muhimmanci ba jam’iyya ba ce, amma irin abin da kake yi wa jama’a.”

By ukarofi