Ana sake duba yafiyar su Maryam Sanda

Spread the love

*Ministan Shari’a ya yi ƙarin haske kan yafiyar Tinubu ga wasu fursunonin Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi ƙarin hasken cewa, babu wani fursuna da aka saki sakamakon yafiya da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi musu a kwanakin baya lokacin bikin ’Yancin Kai, ciki kuwa har da Maryam Sanda, wacce ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), a cikin wata sanarwa jiya Alhamis, yayin da ƙorafi ya yi yawa biyo bayan sakin jerin sunayen mutum 82 da tsare, waɗanda aka yafewa laifukansu.

Idan za a iya tunawa, soke-soke ya yi yawa daga ƙungiyoyi, fitattun mutane, makusanta da ma ’yan adawa kan yadda aka ayyana yafe wa dillalan ƙwaya, masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, masu almundahana da rashawa da masu kisan kai, ciki har da ita Maryam Sanda, wacce ta kashe mijinta, Bilyaminu. A shekara ta 2020 ne aka yanke mata hukuncin kisa bayan kama ta da laifin mijin nata, amma Majalisarr ƙasa ta amince yafe mata a cikin jerin sunayen da Shugaba Tinubu ya miƙa mata.

Daraktan Amnesty International a Nijeriya, Auwal rafsanjani, ya yi allawadai da yafiyar, yana mai cewa, wannan mataki zai zubar da mutuncin Nijeriya a idon duniya kuma zai sanya a riƙa ƙyamar ƙasar.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar yana daga cikin waɗanda suka yi tir da yafiyar, yana mai cewa, hakan ya raunana yaƙi da aikata miyagun laifuka kuma ya ƙarfafa aikata su.

Shi ma Kakakin jam’iyyar adawa da ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya da kuma yin amfani da ikon shugabancin ƙasa ba a wajen da ya dace ba.

Sai dai kuma, Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a Fagbemi ya nemi da kowa ya mayar da wuƙarsa, domin a cewarsa, “har yanzu ba a amince da sakin fursunonin da Shugaban ƙasa ya yi musu afuwa ba.”

Ya yi ƙarin haske da cewa, “kodayake Majalisar ƙasa ta amince da yafiyar, kamar yadda Shugaban ƙasa ya nema, amma akwai matakai na shari’a da mulki, waɗanda dole sai an cika su kafin a saki kowa.

“Da zarar an kammala aikin tantancewar, za a sanar da al’umma jerin fursunonin na ƙarshe da suka cika ƙa’idar a sake su ɗin.”

By ukarofi