Senegal ta shigar da ƙara a CAS bayan CAF ta ƙwace AFCON a hannunta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta ƙasar Senegal (FSF) ta shigar da ƙorafi ga Kotun Shari’o’in Wasanni (CAS) domin ta ƙalubalanci hukuncin Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na ƙwace Kofin gasar ƙasashen Afirka (AFCON) daga gare ta.

CAS ta tabbatar da haka a ranar Laraba inda ta ce an shigar da ƙorafin a hukuncin, wanda ke nuna cewa matakin ya soke rahotannin da ke nuna cewa hukumomin Senegal ba su miƙa ƙorafin nasu ba a lokacin da ya dace.

Al’amarin ya samo asali ne a ranar 17 ga watan Maris, a lokacin da kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya zartar da hukuncin karɓe nasarar AFCON daga ƙasar tare da ayyana Moroko a matsayin wadda ta yi nasara a hukumance.

Wannan mataki ya nuna cewa, Senegal ta taka dokar AFCON sashe na 82 da 84 sakamakon ficewa a fili zuwa ɗakin sanya kaya da ‘yan wasanta suka yi yayin da ake tsaka da buga wasan ƙarshe don nuna adawa da hukuncin alƙalin wasa.

A yanzu dai FSF ta ɗaukaka ƙarar ne a kotun CAS domin sake dawo mara da nasarar da ta samu da fari.

Tuni dai kotun ta ce za ta yi nazari akan ƙorafin cikin girmamawa ga kowane ɓangare tare da tabbatar da yin adalci akan al’amarin.

By Babaji