
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a shirye yake ya yi wa Iran luguden wuta matuƙar ta ƙi amince wa buƙatar tattaunawa akan tsagaita wutar yaƙin da ke tsakaninsu.
A ranar Laraba ne Sakatariyar Fadar White House, Karoline Leavitt ta musanta batun da ke cewa an yi baran-baran a tattaunawar da Amurka ke yi da Iran.
A cewar Leavitt, ana cigaba da tattaunawa kuka ana samun ci-gaba a kai, kamar yadda ta bayyana a wata hira da manema labarai.
Ta ce, akwai ƙamshin gaskiya a game da rahotannin da ke cewa akwai ajanda 15 da Amurka ta shirya akan neman wasu buƙatu daga Tehran, saidai wasu sassan rahotannin ba gaskiya ba ne.
Gidajen jaridun Amurka da Iran sun ce buƙatun sun haɗa da neman Iran ta yarda cewa ba ta da ‘yancin shirya mallakar makaman nukiliya, sannan ta amince za ta lalata dukkan ma’ajiyar makamanta masu linzami.
Kazalika, ta bayyana cewa Shugaban ƙasar ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen yi wa Iran rugugin wuta matuƙar ta ƙi bayar da haɗin kai a batun tsagaita wutar yaƙin Gabas ta tsakiya da ya ƙunshi Amurka da Isra’ila a gefe guda da kuma Iran, inda a yanzu aka shafe kusan wata guda ana gwabzawa.
