Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar SERAP mai rajin kare haƙƙin jama’a da yaƙi da cin hanci ta bayyana cewa ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 5 ga Mayu, 2026, wanda ya umarce ta da biyan diyyar naira miliyan 100 ga wasu jami’an Hukumar Tsaro ta DSS bisa zargin bata suna.
Tun farko dai SERAP ta bayyana hukuncin a matsayin “kuskure da rashin adalci.”
Shari’ar mai lamba Cɓ/4547/2024 jami’an DSS biyu ne, Sarah John da Gabriel Ogundele, suka shigar.
Sai dai SERAP ta bayyana cewa babban lauyanta, Tayo Oyetibo SAN, ya shigar da ƙarar ɗaukaka hukuncin tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar a kotun ɗaukaka ƙara.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce za ta ƙara gyara takardar ɗaukaka ƙarar bayan samun cikakken kwafin hukuncin kotun domin ƙara bayyana kura-kuran da ke cikin hukuncin.
A hukuncin da Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yanke kwanakin baya, kotun ta umarci SERAP da ta biya jami’an DSS ɗin naira miliyan 100 saboda bata suna, tare da bayar da haƙuri a bainar jama’a da kuma biyan naira miliyan ɗaya kuɗin shari’a.
Kotun ta kuma umarci SERAP da ta riƙa biyan kaso 10 cikin ɗari na kuɗin ruwa duk shekara har sai an kammala biyan diyyar.
Sai dai SERAP na ƙalubalantar hukuncin inda ta ce kotun ta dogara ne da wasu hujjoji marasa inganci, ciki har da bayanin shaida da ba a rantse a gaban kwamishinan rantsuwa ba.
ƙungiyar ta ce hakan ya sa hukuncin ya zama mai rauni kuma ya saɓa wa ƙa’idar shari’a.
SERAP ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara da ta soke hukuncin gaba ɗaya tare da watsar da shari’ar saboda rashin cancanta.
ƙungiyar ta ce batun ba wai kan nasara ko rashin nasara kawai ba ne, illa tambayar ko kotu za ta iya yanke hukunci bisa gurɓatacciyar takardar shari’a da kuma hujjojin da ba su cika sharuddan doka ba.
SERAP ta kuma ce kotun ta kasa amfani da ƙa’idar da ake amfani da ita wajen tantance bata suna, inda maimakon duba yadda talakawan gari za su fahimci batun, sai ta dogara da yadda jami’an DSS suka ɗauki lamarin.
ƙungiyar ta ƙara da cewa kotun ta yi kuskure wajen amincewa da sauya sunan wanda aka fara shigar da ƙara a kansa daga ƙungiya mara cikakken matsayi na shari’a zuwa ƙungiya mai rijista.
