Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta kashe fiye da Naira biliyan huɗu wajen biyan kuɗin jarabawar NECO ga ɗalibai a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Daraktar Hukumar Shirya Jarrabawa da Kula da Ayyukan Koyo da Koyarwa ta Jihar Kano (KERD), Hajiya Rabi Inuwa Hussaini, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinta da ke Kano.
Ta ce a shekarar da ta gabata gwamnati ta biya wa ɗalibai dubu ɗari da talatin da bakwai kuɗin jarrabawar NECO, yayin da a bana aka biya wa kusan ɗalibai dubu ɗari da hamsin da bakwai da ɗari bakwai.
A cewarta, wannan mataki ya rage wa iyaye damuwa sosai, musamman a lokacin da ake shirye-shiryen jarabawar kammala sakandare.
Hajiya Rabi ta yabawa gwamnan jihar bisa fifita harkar ilimi, tana mai cewa hakan ne ya taimaka wajen ɗaga martabar jihar Kano a sakamakon jarabawar NECO a shekarar da ta gabata.
Ta kuma yaba wa kwamishinan ilimi da ma’aikatan hukumar bisa jajircewarsu wajen inganta ilimi a jihar.
Daga ƙarshe ta yi kira ga iyaye da ɗaliban da suka ci gajiyar tallafin da su ci gaba da yi wa gwamnati addu’ar alheri tare da mayar da hankali wajen karatunsu domin samun kyakkyawan sakamako.
