Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar masu sayar da shinkafa da sarrafa ta a Kasuwar Kwanar Dawaki da ke Kano.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da su, sabon shugaban ƙungiyar, Alhaji Sham’unu Nasiru Saminu, ya gode wa Allah bisa nasarar da suka samu tare da kira ga ‘yan kasuwar da su ba su cikakken goyon baya.
Ya ce tun bayan zaɓensu ne aka ba su shaidar kama aiki, tare da kira ga gwamnati da ta riƙa tallafawa ‘yan kasuwa domin bunƙasa harkokin kasuwanci.
Sham’unu ya bayyana cewa tun kafa kasuwar shekaru 23 da suka gabata ba a taɓa gudanar da irin wannan taro ba.
Ya ƙara da cewa sun samar da jami’an tsaro domin ƙarfafa tsaro a kasuwar, tare da ƙirƙirar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga hukumar kasuwar.
Haka kuma ya ce suna ƙoƙarin kawar da badala a kasuwar duba da yadda ta ƙunshi matasa maza da mata.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin amintattu na kasuwar, Alhaji Muhammad Sabiu Bichi, ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen bunƙasa kasuwar.
Ya ce sama da matasa dubu goma ne ke cin abinci daga kasuwar saboda yadda ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban ke zuwa sayayya.
Shi ma shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmed Mai Rago, ya yi kira ga ‘yan kasuwar da su haɗa kai domin ci gaban kasuwar.
