Dumamar yanayi: Babura masu ƙafa uku za su koma amfani da batir mai caji

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Matsalar ɗumamar yanayi na daga cikin manyan matsalolin da ke damun duniya baki ɗaya, musamman yadda hayaƙin ababen hawa da masana’antu ke gurɓata muhalli.

Domin magance wannan matsala, wani kamfani mai suna Carbon Asset Nigerian Limited tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya daga ƙasar Ingila mai suna Partnership for Agile Goɓernance and Climate Engagement sun ƙaddamar da wani shiri na mayar da babura masu ƙafa uku zuwa masu amfani da batir mai caji maimakon fetur ko gas.

Shugaban kamfanin a Jihar Kano, Mukhtar Abdulhamid, ya bayyana cewa shirin haɗin gwiwa ne da zai taimaka wajen rage hayaƙin da ke haddasa dumamar yanayi.

Ya ce za su samar da wuraren cajin batirin waɗannan babura domin sauƙaƙa amfani da su.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai da kamfanin ya shirya wa masu gyaran babura da direbobinsu a ɗakin taro na Sa’adu Zungur da ke cibiyar koyar da ilimin siyasa a Mumbayya, Kano.

Mukhtar ya ce shirin zai fara ne a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.

Ya kuma tabbatar wa masu gyaran baburan cewa wannan tsari ba zai hana su aiki ba, sai ma ƙara bunƙasa sana’arsu.

A nasu ɓangaren, shugaban ƙungiyar masu gyaran babura masu ƙafa uku, Malam Musa Muhammad Auwal, ya nuna farin ciki da shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen bunƙasa sana’ar tasu.

Shi ma wani mai gyaran babura, Malam Sani Mato Ibrahim, ya ce sun sha ganin ƙungiyoyi suna zuwa da tsare-tsare iri-iri, amma wannan shirin ya bambanta saboda yadda aka tsara shi.

By ukarofi