Shaharren ɗan fim ɗin nan Olabiyi ya mutu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Fitaccen ɗan wasan Nollywood, Ayobami Mudashir Olabiyi, wanda aka fi sani da ‘Bobo B,’ ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a Ibadan, Jihar Oyo, bayan fama da rashin lafiya na ɗan wani lokaci.

An ce an tsara fitowar shi a wani shirin fim da za a yi a Jihar Oyo a watan da ya gabata, amma bai samu damar halarta ba saboda yanayin lafiyarsa.

Olabiyi ya kwanta asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH), Jihar Oyo, inda daga bisani ya rasu a ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024.

A cikin wata sanarwa, Akinola ta ce, “Muna baƙin cikin sanar da rasuwar sakatare janar na Ƙasa na TAMPAN, Alhaji Mudashir Ayobami Olabiyi ‘Bobo B.’ Allah ya ba iyalansa da dukkan mambobin TAMPAN na duniya haƙurin jure wannan babban rashi. Allah ya jiƙan sa.

By ukarofi