
Daga BELLO A. BABAJI
Duk da kashe-kashe da ɗaiɗaita al’umma da dukiyoyi da Isra’ila ke yi akan mutanen Gaza da wasu sassan ƙasar Palestine, hatta hanyoyin shigar da abinci da magunguna ga ƴan Palestine ya zama abin dakatarwa wanda hakan na faruwa ne bisa goyon bayan Amurka, kamar yadda Ambasadan Palestine a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana.
“Duniya ta ga hotunan marasa lafiya da waɗanda ke gudun hijira sun fake a kusa da asibitin Al-Aqsa da ƙona su da rai. Mata da yara suna shan wahala tare da tsananin ƙona da su ke fuskanta. Babu wata hanya da gaggawa da za a kawo musu ɗauki da za su rayu daga raunukan.”
Abu Shawesh ya ce, a ranar 15 ga watan Oktoba, adadin waɗanda suka rasa rayukansu sun haura 42,227 yayin da masu raunuka suka kai 98,464 waɗanda galibin su mata ne da ƙananan yara.
Adadin waɗanda aka tsare kuwa, sun kai 11,300 a yankin West Bank da Gabashin Jerusalem ciki har da mata 425 da yara 745 da kuma ƴan jaridu 112 waɗanda 59 daga ciki suna kurkuku.
Har’ilayau, mata masu ciki da masu shayarwa na fuskantar rashin kulawa a yankin Gaza.
Kazalika, ya ce Amurka na goyon bayan Isra’ila a idon duniya wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya wanda Isra’ila ta bijire wa akan tsagaita wuta a tsakanin ƙasashen.
