Yaushe Nijeriya za ta gyaru?

Spread the love

Gwamnatin Tinubu tana kan tafarki madaidaici, inji Bankin Duniya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Idan aka yi la’akari da yanayin yadda Tarayyar Nijeriya ke tafiya, za a iya tunanin cewa, daga dukkan alamu babu ranar da ƙasar za ta samu irin cigaba ko ta gyaru kamar yadda akasarin talakawa suke tsammani da fatan samu, illa dai za a iya samun bunƙasa ta fuskar tafiyar zamani, wanda zamanin ne ya zo da shi da kansa, domin masu iya magana su na cewa, an daɗe a na ruwa ƙasa ta na shanyewa.

Yanayin yadda ’yan siyasar ƙasar ke tafiyar gwamnatocinsu tun tale-tale, babu alamun cewa, sun sanya muradun ’yan ƙasa a gaba ko kuma ba su fahimci mene ne muradun ’yan ƙasar tasu ba. Kuma babban abin tsoron shine, ba wai a gwamnatin yanzu ne a ke ganin irin wannan matsala ta ke ba, a’a, magana ce ta gwamnatoci da dama, waɗanda suka shuɗe.

Sai dai kuma wannan ya zo ne a daidai lokacin da Bankin Duniya ya bayyana cewa, matakan da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke ɗauka a Nijeriya suna kan tafarki na daidai. Don haka bankin ya buƙaci Gwamnatin Tarayyar Nijeriyar a ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ta sauya fasalin matakan tattalin arzikin da ta ke ɗauka a halin yanzu, yana mai gargaɗin cewa, hakan na iya haifar da mummunar illa ga arzikin ƙasar.

Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Dr. Ndiame Diop, ne ya bayyana haka jiya Alhamis, 17 ga Oktoba, 2024, a wajen ƙaddamar da rahoton Bunƙasa Nijeriya (NDU) a Abuja, Babban Birnin Tarayyar ƙasar.

Idan dai za a iya tunawa, cire tallafin man fetur da kuma soke tsarin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da wasu yawan manufofin gwamnati mai ci ne ta ɓullo da su tun a ranar farko a ofis, 29 ga Mayu, 2023.

Bankin Duniya dai ya daɗe ya na irin wannan kiraye-kirayen ga Gwamnatin Nijeriya ta fuskar tattalin arzikin ƙasar, lamarin da yawancin ’yan ƙasar ke kallon abin a matsayin wani yunƙuri na hana al’ummar ƙasar rawar gaban hantsi ta fuskar walwala da jin daɗi.

Kodayake ba Bankin Duniya ne ya fara yin irin wannan kira ba ga gwamnatin ta Nijeriya, ita ma Hukumar Bada Lamuni ta Duniya (IMF) ta sha gargaɗin ƙasar da makamancin haka.

Amma a cikin wani bidiyo da wata matashiyar budurwa ta wallafa kuma aka yac shafukan yanar gizo kwanakin baya lokacin da ake zanga-zangar yaƙi da tsadar rayuwa, matashiyar ta yi kira ga ’yan siyasa masu riƙe da madafun iko da cewa, su taimaka su samar mu su abin da za su riƙa, don kada yunwa ta kashe su, in ya so su cinye dukkan sauran dukiyar ƙasar – komai yawanta sun bar musu. Ta ce, yanzu ba maganar samun abin da za su je makaranta ko biyan kuɗin magani, idan sun kamu da ciwo su ke ba, abinci ne matsalarsu kaɗai.

Wannan ya gwada yadda munzalin matsuwar da ’yan Nijeriya suka kai na tsananin fatara da buƙatuwa. Amma duk da haka daga dukkan alamu ’yan siyasar Nijeriya ba su fahimci hakan ba. Ba su gane tasirin abinci ga rayuwar ɗan adam ba. Marigayi Sarki Fahad na Saudiyya ya ce, babbar nasarar da ya samu a mulkinsa ita ce, samar da yanayin da abincin sarki da na talaka iri ɗaya ne a ƙasar; wato kowa zai iya cin shinkafa-kaza ya sha madara.

Wannan ya gwada yadda shugabannin duniya ke bai wa walwalar rayuwar ’yan ƙasarsu muhimmancin gaske, kuma har suke alfahari da cimma nasara kan hakan.

An sani cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana fuskantar matsalolin tattalin da dama, waɗanda suka idan ba a yi da gaske ba, za ta kasa aiwatar da muhimman abubuwan da za su iya durƙusar da tafiyar da su. Kuma kamar yadda muka faɗa a baya, wannan matsala ta daɗe a Nijeriya, ba wai a wannan lokaci ta faru ba.

Za a iya cewa, wannan ne dalilin da ya sa ma jagororin gwamnati ke yawaita jaddada cewa, matakan da suke ɗauka na janye tallafi a muhimman abubuwan more rayuwa, kamar fetur, lantarki, gas da sauransu, matakai ne masu raɗaɗi, amma wajibi ne shugabanni su ɗauke su, don tserar da arzikin ƙasar.

Sai dai kuma abin da suka gaza fahimta shine, fatarar da ’yan Nijeriya suka tsinci kansu a ciki, ta kai munzalin da yunwa ta na kashe su, rashin kuɗin magani ya na kashe su, rashin kuɗin makaranta ya na jefa su a jahilci, jahilci ya na jefa su a halin aikata miyagun ƙwayoyi, kamar ta’addanci, shan miyagun ƙwayoyi da makamantansu. Don haka kenan Nijeriya za ta iya tserar da arzikinta da wannan mataki na janye tallafi, amma ’yan ƙasarta da dama za su iya samun mummunar jikkata.

Babban abin dubawa shine, tun bayan juyin mulki na farko a 1966, sojojin da suka yi juyin mulkin na lokacin Janar Ironsi sun ce gyara za su yi, haka nan waɗanda suka juye shi a ƙarƙashin jagorancin Janar Gowon sun ce sun yi ne don kawo gyara. Shi ma juyin mulkin Janar Murtala an yi shi ne don gyara matsaloli.

Bugu da ƙari, zuwan Janar Obasanjo da miƙa mulki ga Alhaji Shehu Shagari duka an yi su ne don gyara Nijeriya. Haka kuma a lokacin da aka yi juyin mulkin Janar Buhari da na Janar Babangida da ma kafa gwamnatin Cif Shonekan da zuwan gwamnatin Janar Abacha duka sun faru ne da sunan kawo gyara.

Abinda ya biyo bayan kafa gwamnatin Janar Abdulsalami da miƙa mulki ga hannun farar hula a 1999 zuwa yanzu kowanne shi ma shugaba ya na iƙirarin gyara ne fa.

Gyara na nufin tayar da komaɗar abin da ya lalace. Wato kenan ba maganar ainihin ci gaban a ke yi ba, domin ƙasa ba za ta ci gaba ba har sai an gyara ta. Yau an fi shekara 25 da dawo wa mulkin dimukraɗiyya kuma fiye da shekara 64 da samun ’yancin kai, amma har yanzu gyara ake son yi.

Wannan ita ce tambayar da akasarin ’yan Nijeriya suke yi ga Blueprint Manhaja. Mu na fata masu karatunmu za su bayar da amsa daidai fahimtarsu cikin mutuntaka a wannan adireshi [email protected] ko lambar WhatsApp ta 08032875238. Insha Allahu za mu wallafa ra’ayoyin jama’a kan wannan batu a makon gobe.

By ukarofi