Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu mutane uku sun samu raunuka daban-daban a wata fashewa da wata mota mai amfani da iskar gas ta ‘CNG’ ta yi a gidan man NIPCO da ke Unguwar Eyean a hanyar Benin zuwa Auchi a ƙaramar Hukumar Uhunmwonde a Jihar Edo.
Kamfanin Dillancin Labaran iƙna ya ruwaito cewa, ya naƙalto daga shafin Blueprint cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis a gidan mai na NIPCO a lokacin da wata mota ƙirar CNG Audi ke cike da iskar gas.
An kuma tattaro cewa fashewar ta samo asali ne sakamakon wasu na’urorin sauya motar da kuma na’urorin da ba su da inganci da aka yi amfani da su wajen girka man fetur ɗin zuwa gas.
Wani hoton bidiyo mai tsawon daƙiƙa 25 na lamarin ya nuna wata mota da ta lalace bayan fashewar.
An ji wata murya tana cewa an samu fashewar iskar gas a gidan mai na NIPCO.
Rahoton ya ƙara da cewa direban motar ya kasance a gidan mai domin ƙara mai a lokacin da fashewar ta afku.
Muryar ta ƙara da cewa direban motar da ma’aikacin da ya saka kayan aikin CNG a cikin motar, sun je wurin da ake ajiye kaya don gwada ingancin na’urar a lokacin da fashewar ta faru.
Muryar ta yi zargin cewa mutane uku da suka haɗa da na’urar tsaftace tasha, ma’aikacin famfo da ɗaya sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
An kuma bayyana cewa ma’aikacin ya kai ƙarar kansa ga ‘yan sanda inda ya jagoranci tawagar jami’ansa zuwa inda hatsarin ya afku.
Wani ganau da ya zanta da manema labarai, ya alaƙanta fashewar gas ɗin da canza motar daga mai zuwa iskar gas.
A cewarsa, idan ka ga silindar gas da aka yi amfani da shi wajen sauyawar, ya sha bamban da wanda CNG ke amfani da shi.
Da yake mayar da martani, hukumomin NIPCO Gas Ltd. sun danganta fashewar da wani silinda na bogi da mara inganci da aka sanya a cikin motar.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa: “Hukumar NIPCO Gas Ltd. na son sanar da jama’a wani lamari da ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024, a tasharmu ta Compressed Natural Gas (CNG) dake garin Eyean, cikin birnin Benin, jihar Edo.
“Bincikenmu na farko ya nuna cewa fashewar ta faru ne a lokacin da wata mota ta iso domin ɗurs mata iskar CNG. Abin takaici, silindar da aka sanya a cikin motar daga baya an gano ba mai kyau ba ne. Ya fashe bayan an cika shi da kusan 4 SCM na iskar gas.
“Direban motar ya gudu daga inda lamarin ya faru nan da nan bayan fashewar. Duk da yake ba a samu asarar rayuka ba, mutane biyu sun sami raunuka – ɗaya ya samu rauni a ƙafa, ɗaya kuma a a ido. An garzaya da dukkan waɗanda lamarin ya rutsa da su asibiti domin kula da lafiyarsu, kuma ana shirin yi wa ɗaya daga cikinsu tiyata a wani wurin, bisa shawarar likitoci. ƙungiyarmu tana tabbatar da cewa sun samu kulawar da suka dace. “
NIPCO ta kuma bayyana cewa, an kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda na yankin, kuma hukumomi sun cafke jabun silinda da kuma motar da abin ya faru.
