Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rikicin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai wani matsayi mai matuƙar tada hankali, inda aka kashe Falasɗinawa sama da 42,227, yayin da wasu 98,464 suka jikkata, waɗanda galibinsu mata ns da ƙananan yara, ya zuwa ranar 15 ga watan Oktoba.
Halin da ake ciki ya yi muni, inda dubbai suka maƙale a arewacin Gaza, kuma suna fuskantar hare-haren bama-bamai ba dare, ba rana.
A cikin wata sanarwar manema labarai, jakadan ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya yi kira da a shiga tsakani, yana mai jaddada cewa “abu ɗaya tilo da ake buƙata domin cin galaba a kan sharri shi ne mutanen kirki.”
“Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar ɗinkin Duniya OCHA, ya yi Allah-wadai da wannan ɗanyen aiki na ƙona majiyyata da ‘yan gudun hijira a kusa da asibitin Al Aƙsa. Duniya ta shaida abubuwan ban tsoro, amma duk da haka ba a taɓuka komai ba.
“Duk da tashe-tashen hankulan da ake fama da su, jakadiyar Amurka ta musamman Lise Grande ta bayyana cewa, Amurka ba za ta hana Isra’ila makamai ba, lamarin da ya fusata masu rajin kare haƙƙin bil’adama. Wannan matsaya ta sa mutane da yawa suna tantamar rawar da Amurka ke takawa wajen ci gaba da rikicin” inji Abu Shawesh.
Ya ce, “ƙasashen duniya na neman ɗaukar mataki, inda kwamitin bincike na Majalisar ɗinkin Duniya ya yi Allah-wadai da ba Isra’ila haɗin kai.
“ƙwararrun likitocin Amurka 99 da suka yi aiki a Gaza sun rattaba hannu kan wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga shugaban Amurka da mataimakin shugaban ƙasar, inda suka yi bayani dalla-dalla yadda bala’in ya faru. Sun shaida yadda iyaye mata masu fama da tamowa ke shayar da jarirai da gurɓataccen ruwa da kuma mata da ake yi wa tiyata ba tare da an yi musu allura ba.
“Yayin da al’amura ke ƙara taɓarɓarewa, dole ne al’ummar duniya su buƙaci ɗaukar mataki. Dole ne ƙasashen duniya su matsa wa Isra’ila ta ba da haɗin kai ga gudanar da bincike tare da ba da fifiko ga ayyukan jin ƙai. Dole ne Amurka ta sake yin la’akari da goyon bayanta ga Isra’ila tare da yin aiki don ganin an cimma matsaya cikin lumana,” in ji Abu Shawesh.
