Kwamishinan da ke wakiltar shiyyar Arewa maso yamma a hukumar kula da ayyukan majalisar dokoki ta ƙasa (NASC), Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya taya Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, murnar cika shekaru uku a mulki, inda ya bayyana wa’adin gwamnatin a matsayin lokaci na sauyi mai ma’ana da ya sake fasalta jihar Kaduna.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar domin bikin cika shekaru uku na gwamnatin Uba Sani, Hunkuyi ya ce gwamnan ya nuna shugabanci mai hangen nesa da mayar da hankali kan buƙatun jama’a, wanda ya haifar da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.
Ya ce gwamnatin Uba Sani ta samu nasarori a ɓangarorin gine-ginen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa tattalin arziki, tallafa wa matasa da mata, da kuma ci gaban karkara, lamarin da ya kawo sauyi a rayuwar al’ummar jihar.
Ya ƙara da cewa salon mulkin Uba Sani na haɗa kai da kowa, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma kusantar al’umma ya taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a sassan jihar.
Yace “Kaduna na samun sabon salo na ci gaba wanda ke bayyane a fili ga kowa. Ayyukan gwamnati suna bayyane a birane da karkara, kuma hakan ya ƙara wa jama’a gamsuwa kan makomar jihar,”
Tsohon Sanatan ya nuna yaƙinin cewa tubalin da gwamnatin Uba Sani ta kafa cikin shekaru ukun da suka gabata zai ci gaba da kawo ci gaban tattalin arziki, samar da zaman lafiya da kuma ƙara haɓaka rayuwar al’ummar Kaduna nan gaba.
