
Daga UMAR GARBA a Katsina
An gudanar da sallar jan’izar Hajiya Fatima Dada, mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar Najeriya marigayi Mallam Umaru Musa ‘Yar’adua kamar yadda addininin musulunci ya tanada a yau Talata.
An binne marigayiyar ne a kusa da kabarin tsohon shugaban ‘yar’adua a maƙabartar ɗan marna da ke cikin garin Katsina.
Manyan baƙi a ciki da wajen jihar Katsina da suka haɗa da Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima; Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa; ƴan siyasa da sarakunan gargajiya da dai sauransu duk sun samu damar halartar sallar janazar.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, Hajiya Dada ta rasu ne a daren jiya Litinin a asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake Katsina.
Ana kallon marigayiyar mai shekaru 102 a duniya a matsayin uwa da ta haifi wasu daga cikin manyan mutanen da suka jagoranci mulkin Najeriya, duba da cewa ita ce uwa ɗaya tilo a ƙasar nan da ta kafa tarihi inda ta haifi shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna, minista da kuma sanata.
