Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya buƙaci shugabannin ƙasashen duniya da su nemo mafita mai ɗorewa kan yaƙin da ake yi a Gaza, yana mai cewa al’ummar Falasɗinu sun cancanci ‘yancin kai.
Shettima wanda ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya a yayin babban taron majalisar ɗinkin duniya da ake gudanarwa karo na 79 a hedikwatar MɗD dake birnin New York na ƙasar Amurka.
A tuna yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa a Gaza ya fara ne a ranar 7 ga Oktoba, 2023, kuma ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula, tare da mutuwar mutane 1,143 da kuma jikkata wasu dubbai.
Rikicin yana da tushe na tarihi, wanda ya samo asali daga yaƙin kwanaki shida a 1967, wanda ya haifar da mamayar Isra’ila a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan. Rikicin da ba a warware ba tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa ya kasance wani muhimmin abin da ke damun duniya.
Zirin Gaza dai na ci gaba da zama cibiyar tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da yi, inda ake yawan yin musayar wuta tsakanin sojojin Isra’ila da ‘yan ta’addar Falasɗinu, lamarin da ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin fararen hula.
A watan Maris ɗin shekarar 2018, an sake samun tashin hankali lokacin da sojojin Isra’ila suka kashe Falasɗinawa 183 tare da jikkata wasu 6,000 a zirin Gaza.
Da yake jawabi a wajen taron MDD karo na 79, Shettima ya buƙaci shugabannin ƙasashen duniya da su yi tunani a kan rikicin Isra’ila da Falasɗinu, tare da samar da maslaha mai ɗorewa a cikinsa, ya ƙara da cewa rashin yin hakan na nufin ƙasashen duniya sun gaza cimma ruhi da muradun MɗD. don kawar da duniya daga rashin daidaito, tashin hankali da mallake wani da wani.
“A yau, dukkanmu shaidu ne kan halin da ake ciki a Gaza da sauran yankunan Falasdinawa. Ba za mu iya tattauna yaƙi da zaman lafiya ba, rikice-rikice da sulhu ko abubuwan da suka shafi jin kai a yau ba tare da yin la’akari da rikicin Isra’ila da Falasɗinu da ke tashe tun ranar 7 ga Oktoban bara.
“Tabbas, rikicin ya riga ya wuce wannan lokacin kuma yana daɗaɗawa tsawon rabin ƙarni. Abin da wannan ke nuna mana shi ne cewa ƙasashen duniya sun kasa yin aiki da ruhi da muradin Majalisar ɗinkin Duniya na kawar da duniya daga rashin daidaito, tashin hankali da mamayar wata al’umma. Adalci ya saba wa ramuwa.
“Yanci haƙƙi ne da ba za a tauye shi ba, kuma haƙƙi ne na halitta wanda ba za a iya hana shi ga kowa ba. Al’ummar Palasɗinu sun cancanci ‘yancin kansu.
“Sun cancanci samun gida na kansu a yankunan da wannan Majalisar ta amince da su da kuma dokokin ƙasa da ƙasa, wanda aka yi watsi da su akai-akai. Nijeriya na ci gaba da yin kira ga ƙoƙarin da ake na dawo da hanyar da za a bi wajen warware rikicin ‘ƙasashe biyu’ da ke ba da damar samun sabon mafari ga yankin.”
