Shugaban EFCC ya ba da umarnin a binciki zargin da Bobrisky ya yi wa jami’ansu na ƙarɓar miliyan N15

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), Mista Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin karɓar cin hanci da ake zargin wasu jami’an hukumar daga Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a cikin wani bidiyo da ya yaɗu a yanar gizo.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban hukumar ta EFCC Dele Oyewale ya fitar a daren ranar Talata a Abuja, ta ce: “Okuneye, tsohon mai laifi, ya yi zargin a cikin faifan bidiyon da Martins ɓincent Otse wanda aka fi sani da ɓeryDarkMan ya saki cewa wasu jami’an EFCC da ba a bayyana sunayensu ba ne suka karɓi kuɗaɗe N15,000,000 daga gare shi domin a janye tuhumar da ake masa na halasta kuɗaɗen haram.

“A cikin gaggawar mayar da martani, shugaban EFCC ya kafa wata tawagar masu bincike don yin nazari sosai kan zargin. Don haka, Hukumar ta gayyaci duka Okuneye da Otse da su ba da kansu a ofishinta na Legas don taimaka wa masu binciken gano cin hanci da rashawa.

“Hukumar EFCC na son tabbatar wa jama’a cewa za a yi bincike sosai a kan wannan zargi tare da bayyana sakamakon binciken da aka yi a bainar jama’a yadda ya kamata.

“Hukumar ta himmatu ga ainihin kimarta na mutunci, ƙarfin hali, ƙwarewa da haɗin gwiwa a kowane lokaci.”

By ukarofi