Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima tare da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa sun ƙaddamar da babban taron tallafawa ƙanana da matsakaitan masana’antu na ƙasa karo na 9 (Expanded National MSME Clinic) a birnin Katsina.
Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da ci gaban masana’antu, domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar bunƙasa ƙananan ’yan kasuwa a faɗin jihar.
Mataimakin shugaban ƙasa tare da Gwamna Raɗɗa sun ziyarci rumfunan da aka baje kolin kayayyakin MSME, inda suka gana da ’yan kasuwa masu gabatar da sabbin kayayyaki da fasahohi a fannoni daban-daban kamar noma, masana’antu, saka da ɗinki da kuma fasahar zamani.
A matsayin tallafi ga ƙoƙarinsu, kowanne daga cikin ’yan kasuwa 60 da suka nuna kayayyaki a wajen ya karɓi tallafin Naira 250,000 domin bunƙasa kasuwancinsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya yaba da irin jagorancin Gwamna Raɗɗa da jajircewarsa wajen tallafawa matasa da inganta harkokin kasuwanci.
Shi kuma Gwamna Dikko Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na samar da yanayi mai kyau da zai ba damar gina Katsina ta zama jiha mai ƙwarewa, ɗorewa, da dogaro da kai.
A ziyarar sa ta yini biyu mataimakin shugaban ƙasar ya buɗe cibiyar harkokin noma da zai ƙunshi gidan rediyon manoma a harabar ma’aikatan gona da ke sakatariyar gwamnatin jihar.
Shi wannan gidan rediyo idan an kammala zai zama wuri ne na yaɗa manufofin gwamnatin jihar Katsina da ya shafi harkokin noma da kuma ilimintar da manoma da sauraren koken su.
