Shettima ya fice daga rumfar kaɗa ƙuri’a sakamakon rashin ma’aikatan INEC

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima, a yau Asabar ya isa mazaɓar sa ta Shettimari mai lamba 001 a unguwar Lawan Bukar da ke cikin birnin Maiduguri, sai dai ya kasa kaɗa ƙuri’arsa sakamakon rashin isowar kayan aiki da ma’aikatan INEC.

An ruwaito cewa, Shettima ya isa mazaɓar tasa tun misalin goma na safe, sai dai ya tarar da tarin layi na masu jefa ƙuri’a suna tsumayin zuwan ma’aikatan zaɓe tare da kayan aiki, duk da cewa an fara kaɗa ƙuri’a a mazaɓu da yawa da ke faɗin garin.

Ɗan takarar, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran tawagarsa, sun jira kusan mintuna 10 kafin su fice daga mazaɓar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, wato NAN, ya ruwaito cewa, hukumar zaɓe ta kasa INEC ta bayyana cewa, masu kaɗa ƙuri’a 87,209,007 daga cikin 93,469,008 da suka yi rajista sun karɓi katin zaɓe na dindindin, wato PVCs kuma ana sa ran za su kaɗa ƙuri’a.

By Editor