
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar Abuja inda ya tafi Birnin Addis Ababa da ke ƙasar Ethiopiya (Habasha) da nufin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a babban taron Ƙungiyar Ƙasashen African (AU).
Za mayar da hankali ne akan muhimman batutuwan nahiyar Afirka, waɗanda suka haɗa da samar da yanayin kula da lamuran samar da ruwa, inganta lamuran tsabtace muhalli da sauran harkokin ci-gaba da ke ƙarƙashin manufofin AU da take fatan cimmawa zuwa nan da 2063.
Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa akan harkar yaɗa labarai, Stanley Nkwocha a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a ranar Alhamis, ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasar zai haɗu da sauran jagororin ƙasashen nahiyar a taron karo na 39 da kuma babban taron shugabannin ƙasashe karo na 30 da za a yi tsananin ranakun 14 da 15 ga watan Fabrairu, 2026.
A yayin taron, Shettima zai halarci zaman tattaunawa da jagororin siyasa da na kasuwanci da nufin ƙarfafa harkokin difulomasiyyar Nijeriya, tattali, dakarun ƙulla hulɗa da ƙasashen daban-daban na Afirka.
