Gwamnatin Katsina ta raba takardun shedar kama aiki ga sabbin ma’aikatan lafiya 1020

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya ƙaddamar da bayar da takardun shedar kama aiki ga sabbin ma’aikatan lafiya guda 1,020 da ta ɗauka tare da basu horo na kwana biyu.

Ma’aikatan lafiyar, an zaɓo su daga ƙananan hukumomin (34) dake faɗin jihar Katsina, inda kowace ƙaramar hukuma ta amfana da mutane talatin talatin.

Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa” ɗaukar ma’aikatan lafiya yanzu suka fara domin inganta harkar lafiya a faɗin jihar Katsina.

Gwamnan ya yi kira ga sabbin ma’aikatan lafiyar da aka ɗauka da su ji tsoran Allah wajen gudanar da ayyukan su, su kula da marasa lafiya, duba da yadda aka ɗauke su, ba wani ya tsaya masu ba, Allah ne ya zaɓo su.

Shima da yake gabatar da jawabin shi shugaban lafiya matakin farko Dakta Shamsudeen Yahaya ya yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina bisa wannan gagarumin aiki na ɗaukar ma’aikatan lafiya su 1,020 na farko da ya yi wanda ba’a taɓa yin irin shi ba a tarihin jihar Katsina.

Ya kuma yi godiya bisa gudunmawar da suke samu daga gwamnati jihar Katsina, domin inganta ayyukan lafiya a faɗin jihar.

Da yake bayyana yadda ɗaukar ma’aikatan lafiya ya gudana, shugaban kwamitin Alh. Lawal Rufai Safana ya bayyana cewa” kaso saba’in 70% na wanda suka samu nasara ma’aikatan lafiya ne na wucin gadi wanda suka daɗe suna bayar da gudunmuwar su a cikin al’umma.

Alh. Lawal Rufai yaci gaba da cewa” sun gudanar da aikin su bisa chanchanta tare da zaɓo mutanan da suka dace domin basu aikin.

Mutane da dama suka tofa albarkaci bakin su daga ciki akwai shugaban shugabannin ƙananan hukumomin na jihar Katsina Hon. Rabo Tambaya, wasu daga cikin ƙungiyoyin duniya da suke tallafama shirin kiwon lafiya da sauran su.

Bikin wanda ya gudana a babban ɗakin taro na sakatariyar hukumar kula da ma’aikatan ƙananan hukumomin ta jihar Katsina ya samu halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt Hon. Nasir Yahaya Daura tare da wasu abokan aikin shi na majalisa.

Sauran sun haɗa da wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin na jihar Katsina, wakilin mai martaba sarkin Katsina, kwamishina na ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu tare da sauran al’umma.

By ukarofi