Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron CHOGM 2024

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Taron shugabannin gwamanatin Ƙasashen Commonwealth na 2024 (CHOGM), in ji mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, a ranar Lahadi a Abuja.

Mr. Nkwocha, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa Shettima zai haɗe da Sarkin Ingila, Charles, da sauran shugabannin duniya daga ƙasashe 56 mambobin Commonwealth a taron CHOGM da aka shirya za a yi a tsibirin Apia, Samoa, daga ranar 21 zuwa 26 ga Oktoba.

Ya kara da cewa, taron wanda aka sanya wa taken “Gaba Ɗaya Don Makoma Mai Ɗorewa: Sauya Arzikinmu Na Bai Ɗaya ” zai mayar da hankali kan tattaunawa game da yadda Ƙasashen mambobi za su iya amfani da karfinsu ta hanyar jajircewa, buɗe damammaki, amfani da fa’idar Commonwealth, da inganta cuɗanya ta dijital a cikin Ƙasashen Commonwealth.

Haka kuma, ya ce Najeriya da sauran ƙasashen mambobi za su zabi da kuma naɗa sabon Sakatare-Janar na Commonwealth.

By ukarofi