Rundunar soja ta ƙaryata jita-jitar mutuwar babban hafsan sojoji Janar Lagbaja

Spread the love

Hedikwatar Tsaro ta ƙaryata jita-jitar mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Wani shafin X mallakar Jackson Ude, a ranar Lahadi, ya yi ikirarin cewa Babban Hafsan ya rasu a wani asibiti a ƙasashen waje da ba a bayyana ba, kusan sa’o’i 48 da suka gabata.

A cewar wallafar, Lagbaja ya rasu sakamakon ciwon daji na mataki na uku, wanda aka ɓoye labarinsa.

Hakanan, wallafar ta ƙara da cewa ba a sanar da mutuwar Babban Hafsan Sojojin Kasa kai tsaye ba, bisa rahotannin da suka nuna ana gwagwarmayar neman kujerar shugabancin soji da wasu manyan janar-janar ke yi.

Duk da haka, Sojojin Najeriya sun musanta jita-jitar rasuwar Lagbaja ta hanyar shafin su na X @HQNigerianArmy, inda suka bayyana labarin a matsayin “labarin ƙarya”

Rundunar sojan ta bayyana cewa Lagbaja ya tafi hutun aiki kamar yadda kowanne ma’aikaci ya ke da yancin yi.

By ukarofi