Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya soki manufar gwamnatin tarayya ta shigo da abinci daga ƙasashen waje, yana mai cewa hakan na lalata harkar noma a cikin gida kuma yana barazana ga tsaron abinci a ƙasar.
A wata hira da gidan talabijin na News Central jiya, Sarkin ya bayyana cewa, ko da yake yana goyon bayan kusan kashi 80 cikin 100 na manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, amma shawarar shigo da abinci don rage hauhawar farashi tana cutar da manoma kuma tana kawo cikas ga ci gaban noma a ƙasar.
“Idan na fahimta cewa an yanke shawarar shigo da abinci ne domin rage tsadar kaya, amma hakan ya zama akasin abin da ake so. Yana rage ƙwarin gwiwar masu noman cikin gida kuma yana raunana darajar kayayyakin noma,” in ji shi.
Kazalika sarki Sanusi ya yi gargaɗin cewa dogaro da shigo da abinci daga waje zai iya rushe nasarorin da aka samu a gyaran harkar noma, tare da mayar da ƙasar da dogaro ga kasuwannin ƙetare. Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen ƙarfafa noman cikin gida da inganta darajar noma domin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da tsaron abinci.
“Da fatan za mu dawo kan hanya ta gyaran ɓangaren noma — ta hanyar gyara darajar kayan gona da kuma dogaro da noman cikin gida domin ciyar da ƙasa,” in ji shi.
Dangane da yanayin tattalin arzikin kuwa, Sarkin ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa yadda ta yi ƙoƙarin daidaita tattalin arzikin ƙasa ta hanyar haɗa kai tsakanin manufofin kuɗi da na haraji.
“A ɓangaren manufofin kuɗi da daidaito, ba ni da abin cewa sai godiya ga gwamnati,” in ji shi.
“Amma ɓangaren haraji kuwa mun ga ƙarin kuɗaɗen shiga idan aka kwatanta da GDP, na rage yawan bashin da ake biya, da kuma taƙaita giɓin kasafin kuɗi. Waɗannan duk abubuwa ne masu kyau, amma har yanzu akwai doguwar tafiya.”
Sai kuma, tsohon gwamnan na CBN ya nuna damuwa kan yadda kuɗaɗen gwamnati ke ta ƙaruwa da kuma tsadar gudanar da mulki.
“Ina ganin akwai buƙatar a sake nazari sosai kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati. Har yanzu muna kashe kuɗi da yawa wajen gudanar da mulki — akwai masu muƙamai da yawa, da jami’ai da yawa.”
“Idan ba mu inganta yadda ake kashe kuɗi ba, kuma ba mu rage yawan kashewa ba, za mu ci gaba da cin bashi.”
Sanusi ya yi gargaɗin cewa Najeriya na iya komawa cikin tarkon bashi idan gwamnati ta gaza sarrafa kuɗaɗen da aka ce na cire tallafi ne yadda ya kamata.
Duk da irin waɗannan damuwoyi, Sarkin ya yaba da ƙoƙarin gwamnati, yana mai cewa gaba ɗaya, tafiyar da ake yi tana kan madaidaiciyar hanya.
“Gaba ɗaya, zan iya cewa kusan kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na abin da gwamnati ke yi da alkiblar da take bi, ina goyon bayansu,” in ji shi. “Abin da kawai nake da shakku a kai shi ne batun shigo da abinci da kuma yadda ake kashe kuɗaɗe, amma gaba ɗaya muna tafiya a hanya mai kyau.” inji Sarkin na Kano
