Gwamna Raɗɗa ya yaba wa sojin Nijeriya bisa tunkarar matsalar tsaro

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Mallam Dikko Umar Raɗɗa ya yabawa rundunar sojin Nijeriya bisa namijin ƙoƙarin da suke yi na tunkarar ƙalubalen tsaro a Katsina da ma ƙasar baki ɗaya.

Gwamna Raɗɗa ya yi wannan yabon ne a yayin wata ziyara da ya kai wa babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Olufemi Oluyede a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ta fitar ranar Alhamis.

Gwamnan ya yaba da ƙwazo da jajircewa da sojojin da ke yaƙi da ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Katsina, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da suka yi ya haifar da ci gaba a harkar tsaro.

Ya kuma yaba wa babban hafsan sojojin bisa yadda yake ci gaba da baiwa rundunar goyon baya da kuma ziyarar da ya kai Katsina a baya-bayan nan, wanda ya ce hakan ya ƙara ƙwarin gwiwar jami’an da ke aiki a jihar.

Gwamnan ya bayyana shirin gwamnatinsa na yin haɗin gwiwa da rundunar soji wajen kafa wani ƙarin sashi a jihar domin ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro.

Ya kuma amince da haɗin kan tsaro tsakanin Katsina Community Watch Corps (Jami’an tsaron al’umma na gwamnatin jihar) da sojoji, inda ya ce irin wannan haɗin kai shine mabudin murƙushe masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya.

Kazalika, Mista Oluyede ya gode wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai masa, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da jajircewar rundunar na kare ‘yan ƙasa daga nan sai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda don samar da ingantaccen yanayin tattalin arziki.

Ya kuma yabawa gwamnati da al’ummar Katsina bisa irin goyon bayan da suke baiwa sojoji a ko da yaushe, daga ƙarshe babban hafsan sojin ya yi kira da a ci gaba da bayar da haɗin kai wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro.

By ukarofi