Shirye-shiryen zaɓen shugabannin APC na shiyyar Arewa maso Yamma a Kaduna ya yi nisa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kaduna

Ayyuka sun fara gudana cikin tsari a dandalin Murtala Square da ke cikin Kaduna inda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke gudanar da zaɓen shugabanninta na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shirye-shiryen gudanar da zaɓen sun yi nisa matuƙa domin tabbatar da cewa komai ya tafi cikin tsari, lumana,tsaro da nasara.

A halin yanxu gurin taron ya karɓi ɗimbin jiga-jigan jam’iyya, wakilai da magoya baya daga sassa daban-daban na yankin, lamarin da ya haifar da yanayi na farin ciki, fatan alheri da kyakkyawan zato kan sakamakon zaɓen.

Mahalarta taron na ci gaba da zuwa cikin tsari ,suna musayar ra’ayoyi tare da nuna ƙwarin gwiwa kan ingancin tsarin zaɓen.

Jami’an tsaro sun bazu a muhimman wurare domin tabbatar da zaman lafiya da kare lafiyar mahalarta taron, yayin da jami’an gudanar da zaɓe ke cigaba da kula da dukkan matakai domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Ana sa ran wannan zaɓe zai ƙara ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar a yankin, tare da inganta tsarin shugabanci da kuma kara mata ƙarfin tasiri a siyasar Arewa maso Yammacin Najeriya.

By ukarofi