Mohamed Salah zai bar Liverpool a ƙarshen kakar bana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Birtaniya sun nuna cewa tauraron ɗan ƙwallon Misra, Mohamed Salah ya shirya barin ƙungiyar Liverpool bisa yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu.

Liverpool ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo a ranar Talata, inda ta ce zaman Salah ƙungiyar zai zo ƙarshe a ƙarshen kakar 2025-2026.

Wannan ya nuna cewa ɗan wasan ya amince da ficewa daga ƙungiyar bayan shekara tara yana wakiltar Liverpool a wasannin gasa da dama da take ciki.

Salah a nasa ɓangaren, ya yi godiya ga magoya bayan ƙungiyar bisa damar da ya samu a Liverpool yayin da ya ƙudiri aniyar sauya sheƙa domin gobensa.

A shekarar 2017 lokacin bazara ƙungiyar ta sayo zakaran ɗan ƙwallon daga AS Roma ta ƙasar Italiya, inda tun daga lokacin zuwa yanzu ya zama ɗaya daga cikin gwarazan ‘yan wasa da Liverpool ta yi a tarihinta.

Ɗan Misran ya taimaka mata wajen lashe kofin gasar Premier League sau biyu, Champions League ɗaya, FIFA Club World Cup ɗaya, UEFA Super Cup ɗaya, FA Cup ɗaya, kofunan Carabao da kuma FA Community Shield.

Haka kuma a wasanni 435 da ya wakilce ta, ya zura jimillar ƙwallaye 255 zuwa yanzu, wanda ya sa ya zama na uku cikin ‘yan wasa mafiya zura ƙwallo a tarihin ƙungiyar, lamarin da kuma ya sa ya lashe Premier League Golden Boot sau huɗu.

Kazalika, Salah yana da wasu nasarori da ya samu yayin wakiltar ƙasarsa Misra da kuma waɗanda ya samu a karan kansa.

By Babaji