Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da samun damar ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Allah Ya barɓi ibadunmu na wannan wata mai alfarma, Ya sa mudace, Ya sa mun dace.
Harwayau dai muna nan kan darasinmu na waken soya, wanda yau ya kasance sati na uku akan darasin.
Kun dai ji a baya mun bayyana sinadarai da ke tattare a cikin wannan abunci da Allah ya azurta mu da shi, da kuma irin tasirinsa a lafiyar fatarmu tare kuma da yadda ayyukan waɗannan sinadarai ke kama da aikin sinadarin halitta da ke aikin ba wa fata kariya a wasu ɓangarori.
Kuma kun ji yadda waken soya ke taimaka wa fata a lokacin da ta fara gazawa sakamakon shekaru.
Kasancewar duk abinda muka faɗa a baya ba ra’ayi ne na mu ko na wani mutum ɗaya ba, ba kuma ƙirƙira aka yi ba, masana ne suka faɗa, su ma kuwa sai da suka yi dogon bincike ciki kuwa har da gwaje-gwaje don tabbatarwa kafin su faɗa, sakamakon tasirin kalamansu a matsayinsu na masana.
Da wannan ne shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja ya waiwaye wasu daga cikin gwaje-gwaje da aka yi kan shi waken soya da irin sakamakon da aka samu.
Binciken mata a ƙasar Japan:
An gudanar da wani bincike kan mata 26 inda aka ba rabin su sinadarin soya tsawon makonni 12.
Sakamakon ya nuna:
1. Raguwar layukan fata da tsufa ke haddasawa.
2. ƙaruwa a laushin fata.
3. Babu wata illa da aka samu sakamakon shan da suka yi.
Bincike kan mata bayan daina jinin al’ada:
A wani bincike da aka yi tsawon watanni shida, an ba wasu mata haɗin sinadaran soya da wasu tsirrai da sinadarin bitamin.
Sakamakon ya nuna;
1. Raguwar layukan fuska na tsufa.
2. Raguwar duhun zagayen ido.
3. Samun kyawun fata da sheƙi fiye da kafin shan.
Duk da cewa, masanan sun ce, waken soya kaɗai ba zai ɗauke alhakin duka sauyin da aka samu a wannan binciken ba, kasancewar an haɗa shi da wasu sinadaran
