Kwanon maigida daban da na ‘yan gida

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

Masu karatu idan ku na biye da mu, kun ji yadda baƙuwarmu ta koro bayani kan wannan darasi na mu, ta bayyana asali da kuma yadda wannan ɗabi’a ke tasiri ga tarbiyya da kuma dukiyarmu. A wannan satin za mu ba ta dama don ta kawo mana mafita kan wannan matsala, domin dai an ce babu damuwar da ba ta da magani, ko a hannun mutum ko ta wurin wanda ya yi mutum. SA’ADATU SAMINU KANKIA ce a shafin na iyali:

Ta yaya kike ganin za a iya shawo kan wannan matsala?

Abu ne mai sauƙi Hajiya Aisha, idan dai maza za su ɗauki aure matsayin ibada, su yarda iyalinsu nauyi ne, su amana ce Allah Ya ɗora ma su, sannan su yarda cewa duk abinda za su yi ma iyalinsu na haƙƙoƙin rayuwa wajibi ne a kansu, sannan su yarda cewa wata rana ƙarfinsu za ya ƙare, za su dawo ƙarkashin waɗannan ‘ya’yan. To tabbas za a samu gyara. ina ƙara faɗi, ba cin abincin waje ne laifi ba, rashin wadata iyalai ne babbar matsala.

Akwai wata matsalar ma za ki ga wani baya ci wajen, amma a cikin gidan abincinshi daban da na iyali, shi ga miya ga nama, su kuma su ci da mai. Yaro fa ba ya mantuwa, wannan abin da kake ganin ba matsala ba ce yana nan yana tasiri a tunaninshi, ko dai ya kasa taimaka ma ka lokacin da kake buƙatar taikamon, ko kuma shima ya yi ma na shi iyalin haka.

Wannan shi ne bambancin uwa da uba, babu yadda za a yi uwa ta zauna gaban ɗanta ta ci abu mai daɗi ta hana ɗanta.

Daga ƙarshe, wane kira za ki yi ga magidanta masu irin wannan hali?

Shawara ta ɗaya ce, su sani, iyalinsu amana ce a hannunsu. Kuma sai kun kyautata masu su ma za su tausaya ma ku lokacin da ƙarfinku ya ƙare. Ku sani shi aure ibada ne, duk abinda ka yi ma iyalinka Allah na sane, kuma za ya yi ma ka sakayya, za Ya buɗa ma ka. Sannan duk abinda za ka samu, akwai haƙƙin iyalinka a ciki, Allah da ya raba arziki Ya ba ka, Ya ba ka har da na iyalinka ne, don haka maza ku ji tsoron Allah, ku yi ƙoƙarin gyarawa. A kamanta. Allah ya bada ikon gyarawa ya wadata mu da arzukinshi, Amin.

MANHAJA: Aure ba ya wajaba kan namiji har sai da cikar wasu sharuɗɗa; lafiyar da za ka iya sauke haƙƙin aure ta ɓangaren auratayya, sana’a ko aiki da zai iya ciyar da matar da za ka aura, muhallin da za ta zauna. 

Idan aka rasa ci da sha wanda shi ne a layin farko, to fa ragowar sharuɗɗan ba sa iya kore shi. Idan har ba ka da abin da za ka iya kula da matarka, musamman ta ɓangaren abinci, to ko ka na da lafiya, Musulunci bai ba ka damar ajiye mata ba. Abinda aka ce sai dai ka yawaita azumi har lokacin da ka samu zarafin auren.

Idan mun fahimta, za mu amince cewa babu hujjar da zai sa ka auri mace alhali ba ka da abin kula da ita. Sai dai idan ku na tare rashin ya riske ka, wannan kam Musulunci ya so ta yi haƙuri ta zauna, amma fa idan ta ji ba za ta iya ba, babu laifi gareta idan ta nemi rabuwa.

Da yawa maza na ɗaukar sha’anin ciyarwa da wasa, abin da ba su sani ba zai iya zama sanadiyyar shigarsu wuta idan har suka sa ganganci a ciki. Addini ya sanar da ku cewa, ku ciyar da su(matanku) da abin da ku ka ci, ku tufatar da su idan kun tufata. Don haka babu inda ya halasta ga maigida ya fifita kwanonsa akan na iyalansa.

By ukarofi