Tare da BILKISU YUSUF ALI
Aure yarjejeniya ce ta zaman tare na iyali wanda ake sa ran kwanciyar hankali da nutsuwa cikinta. Babbar ribar da ake fata da an yi aure ita ce samun iyali; iyali kuwa nagartattu su ne abin nema, don gina rayuwar al’umma masu tasowa. Mata sune ginshiƙi na kula da gida da ma maigidan da ‘ya’yan gida da ma duk wani wanda ke mu’amala da gidam. Mace da ke fita aiki sawa’un aikin nan na gwamnati ne ko kuma akasin haka tana da ƙalubale inda wasu ke hangen wannan fita da ta ke yi abu ne na larura da taimakon kai wasu kuma a hangensu sam mace ta zauna a gida shi ne ma fi a’ala da dacewa.
Duk matar da mijinta ya bar ta aiki ya kamata ta zama kamar haka:-
Kamun kai
Kamun kai yana da matuƙar muhimmancia gun kowacce mace tun daga kan marar aure bare kuma wadda take ta mallakin hankalinta har take da igiyar aure. Ana gane mace marar kamun kai ta hanyoyi da dama ciki akwai:-
Surutu barkatai
Za a ga wata matar rau-rau harshenta ya karaɗe ko’ina a wajen aiki ba a wajen abokanan aikinta mata har a waje mazan ta zama tamkar radiyo in ta fara zuba abinda aka tambayeta da ma wanda ba a ma saka ta ba duk za ta yi uwa ta yi makarɓiya.
Ciye-ciye
Duk macen da za ta zama a gaban kowa za ta hau ciye-ciye to fa tana da matsalar kamun kai.
Sanya sutura mai nuna tsiraici shi ma wani salo ne na nuna rashin kamun kai. Duk mace ta kwarai ya zama wajibi ta sanya sutura wadda za ta rufe jikinta ruf
Roƙo
Roƙo hanya ce ta nuna rashin kamun kai . Wasu matan suna da ɗabi’ar roƙe-roƙe a hannun maza wanda wannan roƙo shi zai ba da hanyar abubuwa da dama su shigo na raini ko maganar banza.
Gori
Maza da dama ba aikin mace ne ba sa so ba sai dai gudun gori. Akwai mata da duk abinda suka yi wa miji ko danginsa ko ma yaransu sai su goranta wanda wannan ba karamin naƙasu ba ne
Yawo
Wata matar ba ta gajiya da fita . Bayan yarda da mijinta ya yi da ita ya bar ta take fita aikin kuma sai ta ƙirƙirarwa kanta wani sabon yawon it ace kasuwa ita ce yawon biki da suna har da ma inda bai dace t aje ba kuma da aikin za ta fake ta je.
Rashin mayar da hankali ga al’amuran gida
Akwai mata da dama da in suna aiki kuma sai su kawar da kansu ga duk wani na mazajensu kama daga gyaran gida zuwa abinci da ma kula da tsaftar yara da tarbiyyarsu. Akwai wasu matan da in suna aiki rayuwar ‘ya’yansu da tarbiyyarsu ta koma hannun makwabta ko masu aiki.
Gadara/wulaƙanci
Wata matar kuwa don ta ga tana aiki tana ɗaukar albashi sai ta zama tsakaninta da mijinta sai Gadara da wulaƙanci hatta dangin miji za ta ke kallonsu ba a bakin kome bas hi kansa biyayya da Allah ya wajabta mata ta yi masa sai ta gagara .
Barin wata kafa da za a yi zargi
Sau tari mata su ke barin wata kafa ko su ɗarsawa mazajensu wani abu da zargi zai biyo baya. misali ta dawo gida da wani abu na abokin aikinta wanda bai ma shafi aikin ba ko kuma a dawo gida a shiga yin waya ana hira ko kuma ba da wata kulawa ta musamman.
Wannan da ma wasu dalilai su ke sa wa maza na tsoro ko kuma suna kyamar mace mai aiki. Aikin mace na da fa’ida kwarai kuma ba lallai sai ma aikin baa bin da aka fi buƙata wanda ya zama wajibi shi ne a samarwa mata abin yi. Akwai sana’oi da mata za su iya aiwatarwa a cikin gidajensu wanda iyayenmu da kakanninmu ke yi kuma sun yi rayuwa mai kyau sun amfani kansu sun amfani wasu.
Mace in tana aiki ya kamata ta zama mai nutsuwa da sanin ya kamata da kyautatawa. Duk abinda mace za ta yi ta fara sa tsoron Allah a gaba ta tsayar da haƙƙin Allah. Duk matar da mijnta ya bar ta ta yi aiki ko sana’a to fa ya wuce gori ko wulaƙanci ko rashin biyayya don zalunci ne saka alkhairi da sharri.
Haƙƙin maigida ne ɗaukar ɗawainiyar dukkan gidansa amma kyautatawace idan kina aiki ki taimakawa maigida ko da kuwa yana da shi. Kada ki sa ido a al’amuransa sannan ‘yan’uwansa ki kyautata musu wannan alamu ne na tukwici ga abinda ɗan’uwansu ya yi miki na barinki ki nemi naki.
