Shugaba Putin ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine

Spread the love

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a ranar Ista da kuma ranar Lahadi, Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura.

Ƴan lokuta bayan da Shugaban Rasha ya sanar da haka,Volodymyr Zelensky shugaban Ukraine ya mayar da martani ta hanyar yin tir da “yunƙurin Putin na wasa da rayukan mutane,” ba tare da bayyana matsayin ƙasarsa a fili kan tsagaita wutar ba.

Rasha ta kuma yi iƙirarin cewa ta kusan kwato yankunan da sojojin Ukraine suka mamaye tun lokacin bazarar a shekara ta 2024 a yankin Kursk da ke kan iyakar Rasha. ƙasashen duniya na ci gaba da kira na ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙi, duk da cewa Rashan da Ukraine kowanensu na iƙirarin samun galaba a yaƙin.

By ukarofi