Shugaban ƙaramar hukumar Augie ya ƙaddamar da yasar magudanun ruwa

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya ƙaddamar da aikin yasar magudanun ruwa a manyan garururwan da ke ƙaramar hukumar. Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da aikin a garin Augie, Honarabul Yahaya Muhammed ya ce wannan yana daga cikin ayyukan da ya kamata a fuskanta saboda kaucewa barazanar ambaliya saboda masana sun yi hasashen akwai yiyuwar ambaliya a wannan daminar.

Ya ƙara da cewa ko ba komai dai yana da kyau mutane su tsaftace muhallin su saboda gudun kamuwa da cututtuka musamman a yanayin damina. Ya nemi magidanta da su bai wa wannan shirin goyon baya don samun nasarar kammala shi cikin lokaci sannan kuma su daina zuba shara a cikin magudanun ruwa musamman a lokacin rani wanda shi ne ke haddasa cunkushewar magudanun ruwa har ya yi sanadiyyar ambaliya cikin gidajen mutane.
Da ya ke jawabi a madadin mutanen anguwar, Malam Ibrahim ya yaba wa wannan tsarin na Honarabul Yahaya Augie inda ya ce wannan aikin ya zamo bazata saboda an yi shugabanni a baya amma ba su taɓa samun haka ba. Ya kuma bayyana cewa za su kula da magudanun ruwan ko bayan damina ta hanyar hana zuba shara a ciki.

By ukarofi

Leave a Reply