Shugaban Iran ya fitar da sunayen mutum uku da za su gaje shi idan ya mutu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana wasu malamai uku a matsayin masu yuwuwar maye gurbinsa, a wani mataki na gaggawa da ya ɗauka sakamakon barazanar kisa daga Isra’ila. Jaridar New York Times ta ruwaito cewa Khamenei, mai shekaru 86, yanzu yana ɓuya a wani mafakar ƙasa a birnin Tehran kuma baya amfani da kayan sadarwa na zamani, sai dai ta bakin amininsa.

Bayan hare-haren da Isra’ila ta kai da suka kashe manyan jami’an sojin Iran, hukumomi sun tabbatar cewa tsarin shugabanci na ƙasar bai ruguje ba. A cewar majiyoyi, Khamenei ya tanadi jerin sunayen wasu sabbin shugabannin soja idan har akwai sauran kashe-kashen manyan hafsoshin tsaro. Sai dai ɗansa Mojtaba, wanda ake ganin zai gaje shi tun bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Raisi a hatsarin jirgin sama, bai cikin waɗanda aka zaɓa.

Majiyar Iran International ta ce Khamenei da iyalansa sun koma wata mafakar ƙasa a yankin Lavizan, amma wannan rahoton bai samu tabbatarwa daga wasu hukumomi masu zaman kansu ba. A halin yanzu, shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce ya dakatar da wani yunkurin Isra’ila na kashe Khamenei tun ranar farko ta yaƙin. Ya kuma ce yana sane da inda Khamenei yake, amma yana jiran lokaci daidai kafin yanke hukunci kan harin nukiliya.

Yayin da rikicin ke ƙara tsananta, Khamenei na ƙoƙarin tabbatar da cewa an samar da daidaito a cikin ƙasar ta hanyar saiti da tsarin maye gurbinsa kafin wani mummunan abu ya faru. Masana da dama sun bayyana cewa wannan matakin zai iya hana rikicin cikin gida da kuma tabbatar da ci gaba da dawwamar da iko a lokacin yaƙi.

By ukarofi