Daga DAUDA USMAN a Legas
Shuwagabannin Kasuwar Mile-12 dake birnin Legas a ƙarƙashin jagorancin babban shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam, Sardaunan Egbaland Abeokuta ta Jihar Ogun sun bayyana cewar sun yi na’am da ziyarar mai martaba Alhaji Ibrahim Hamza Bayaro ɗanmajen Kano Hakimin ƙiru ya kawo masu a Legas.
Alhaji Shehu Usman shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da shi da sauran shuwagabannin ɓangarorin kasuwar suke gudanar da taron karɓar baƙuncin babban baƙon su mai martaba Alhaji Ibrahim Hamza Bayaro, wanda kuma shine ya kasance Hakimin ƙiru.
Taron ya ƙunshi dukkan shuwagabannin kasuwar ta Mile-12 da iyayen ta da sauran masu ruwa da tsaki bisa kan harkokin kasuwanci a kasuwar gabaɗaya.
Hakazalika taron ya gudana a harabar babban ofishin kasuwar dake Unguwar Mile-12 Legas Alhaji Auwalu ƙiru kuma shugaban matasan ƙaramar Hukumar ƙiru shine ya gabatar da sunayen shuwagabannin kasuwar tare da muƙamansu a wajen taron. Hakazalika shugaban matasan na ƙiru ya cigaba da bayyanawa babban baƙon irin kyakkyawan jagorancin da al’ummar ƙiru suke samu da sauran ‘yan kasuwar a wajen shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam.
Haka kuma shuwagabannin kasuwar sun gabatar da jawabansu ɗaya bayan ɗaya inda suka nuna farin cikinsu da jin daɗi dangane da wannan ziyara ta ɗanmajen Kano a Legas.
Shi ma a nasa tsokacin a wajen taron, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam ya tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan al’amarin inda bayan ya kammala yi wa babban baƙo da tawagar sa barka da zuwa ya cigaba da bayyana kaɗan daga cikin tarihin kasuwar inda ya ce a sakamakon kasuwar ta Mile-12 Intanashinal maket a legas Marigayi Alhaji Muhammadu mai dankalin Turawa ɗan asalin ƙaramar Hukumar ƙiru ne ya assasata kuma Dakta Alhaji Ibirahim Hamza Bayaro ɗanmajen Kano shine basarake na farko daga arewacin Nijeriya wanda ya fara kawo wa wannan kasuwar ta Mile-12 ziyara kuma ya kasance ɗan asalin ƙaramar Hukumar ƙiru in ishi, bisa ga haka a sakamakon jin daɗin wannan ziyara da ɗanmajen Kano ya kawo masu a Legas a cewarsa daga wannan lokaci sauran “yan kasuwar sun koma ‘yan asalin ƙaramar Hukumar ƙiru gabaɗaya.
ɗanmajen Kano ya yi jawabin godiya ga ‘yan kasuwar bisa ga karamcin da suka yi masa a wajen amsar baƙuncinsa a Legas.
