
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Ungozomomi ta Ƙasa (NANNM) da Cibiyoyin Lafiya na Tarayya sun musanta rahoton da ya karaɗe kafafen yaɗa labarai cewa sun dakatar da yajin aikin gargaɗi da suka tsunduma kwanaki kaɗan da suka gabata, ranarJuma’a.
A ranar Laraba aka shiga yajin aikin wanda a cewar ƙungiyar kwamitin zartarwarta ke da alhakin sanar da dakatarwar duba da cewa akwai zama da zai yi a yau Asabar, kamar yadda kakakin ƙungiyar Omomo Tibiebi ya shaida wa manema labarai.
Hakan ya biyo bayan kalaman Ministan Ilimi, Farfesa Muhammad Pate na cewa an dakatar da yajin aikin a ranar Juma’a.
Farfesan ya bayyana hakan ne jim-kaɗan bayan wata ganawar sirri da jagororin ƙungiyar a ranar.
Saidai, da ya ke magana, kakakin ƙungiyar ya ce ministan ba shi da hurumin sanar da janye yajin aikin saboda a cewarsa, ba shi ya kira aka tsunduma ba.
Ungozomomi sun shiga yajin aikin ne bayan wa’adin da suka bai wa gwamnati na ta amsa buƙatunsu ya ƙare a tsakiyar watan Yuli, 2025 ba tare da sakamako ba.
