Shugabannin Sin da Amurka sun gana yau a Bali

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun gana a yau Litinin, gabanin taron ƙolin ƙungiyar G20 da zai gudana a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia.

A cewar Xi Jinping, ya kamata ƙasashen biyu su waiwayi tarihi, kuma ya zama alƙiblar da za su bi a nan gaba.

Ya ce yanayin da ake ciki yanzu game da dangantakar Sin da Amurka, bai dace da moriyar ƙasashen biyu da al’ummominsu ba, haka kuma bai dace da fatan al’ummar ƙasa da ƙasa ba.

Kuma a matsayinsu na shugabannin manyan ƙasashe biyu, ya kamata su lalubo hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu.

Ya ƙara da cewa, al’ummun ƙasa da ƙasa na sa ran ganin Sin da Amurka sun tafiyar da dangantakarsu ta hanyar da ta dace, yana mai cewa, ganawarsu ta yau, za ta ja hankalin duniya baki ɗaya.

A don haka, ya kamata su hada hannu da sauran ƙasashe wajen ƙara fatan wanzuwar zaman lafiya a duniya, da ƙwarin gwiwa kan kwanciyar hankalin duniya da ingiza ci gaba na bai ɗaya.

Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce yana sa ran haɗa hannu da shugaba Biden domin mayar da dangantakar ƙasashen biyu bisa turbar da ta dace da samun ingantaccen ci gaba domin moriyar ƙasashen biyu da ma ƙaukacin duniya.

“Haƙƙinmu ne nuna cewa, Sin da Amurka za mu iya haƙuri da bambance-bambancen dake tsakaninmu da kaucewa riƙidar takara zuwa rikici, da lalubo hanyoyin haɗin gwiwa kan muhimman batutuwan duniya.

Da ni da Xi, muna sa ran ci gaba da tattaunawa bisa gaskiya ba tare da rufa-rufa ba kamar yadda aka yi a baya,” a cewar Shugaba Biden.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha