An jinjinawa matakan Sin na shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi

Daga CMG HAUSA

Mahalarta taron sauyin yanayi na MƊD dake gudana yanzu haka, sun jinjinawa matakan da ƙasar Sin ke aiwatarwa game da shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi.

Da yake tsokaci game da hakan, babban jami’in cibiyar ƙasa da ƙasa mai lura da aiwatar da matakan shawo kan sauyin yanayi Patrick Verkooijen, ya ce cikakken shirin shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi na ƙasar Sin ya ciri tuta.

Ya ce Sin ce kaɗai ƙasar da ke maida hankali matuƙa game da yanayin da ake ciki yanzu, da kuma damammakin gobe a fannin sauyin yanayi.

A nasa ɓangare kuwa, mashawarci na musamman ga babban sakatare, da mataimakin sakataren MƊD mai lura da batun sauyin yanayi Selwin Hart, cewa ya yi aiwatar da matakan shawo kan sauyin yanayi, wanda shi ne babbar matsala ga ƙasashe masu tasowa, ya jima da zama rabin kaso na ƙalubale da kasashen ke fuskanta ta fuskar sauyin yanayi.

Jami’in ya ce salon da ƙasar Sin ke aiwatarwa yana amfanar ƙasar, yana kuma ba ta damar raba ƙwarewa da sauran sassan, da faɗaɗa haɗin gwiwa da sauran ƙasashe masu tasowa.

Shi ma mataimakin shugaban bankin raya nahiyar Asiya Ahmed Saeed, jinjinawa salon shawo kan sauyin yanayi na Sin ya yi, wanda ya ce kyakkyawan mataki ne dake daga matsayin hadin gwiwar ƙasa da ƙasa, mai tasiri wajen shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi.

Mai fassara: Saminu Alhassan