Sojojin Nijeriya sun fitar da jerin sunayen ’yan ta’addan da su ke nema ruwa-a-jallo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Tsaron Nijeriya ta fitar da sunayen mutum 19 waɗanda ta ce ’yan ta’adda ne a ƙasar kuma tana neman su ruwa-a-jallo.

A sanarwar da ta fitar ranar Litinin, rundunar ta ce, mutanen sun daɗe suna tafka ɓarna a Arewa maso Gabas, da arewa maso yamma da kuma arewa maso tsakiyar ƙasar ta Nijeriya.

Ta kuma ce, duk wanda ya bayar da bayanin da ya taimaka wajen kama kowanne daga cikin mutanen za a ba shi tukwicin naira miliyan 5.

Sunayen mutanen, kamar yadda daraktan yaɗa labaru na cibiyar tsaron na Nijeriya Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar su ne:

  • SANI DANGOTE – Dumbarum, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.
  • BELLO TURJI GUDDA – Fakai, jihar Zamfara.
  • ALHAJI ADO ALIERO – Yankuzo, ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
  • MONORE – ’Yantumaki, ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina.
  • LEKO – Mozoji, ƙaramar hukumar Matazu, jihar Katsina.
  • DOGO NAHALI – ’yar tsamiyar jino, ƙaramar hukumar Ƙanƙara, jihar Katsina.
  • ISIYA KWASHEN GARWA – Kamfanin Daudawa, ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina.
  • GWASKA DANKARAMI – Shamushele, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.
  • HALILU SUBUBU – Sububu, ƙaramar hukumar Maradun, jihar Zamfara.
  • NASANDA – Kwashabawa, ƙaramar hukumar Zurmi, Jihar Zamara.
  • ALI KACHALLA, wato ALI KAWAJE – Kuyambana, Dansadau, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.
  • BALERI – Ƙaramar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.
  • NAGONA – Angwan Galadima, ƙaramar hukumar Isa, jihar Sakkwato.
  • ABU RADDE – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.
  • DAN-DA – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.
  • MAMUDU TAINANGE – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.
  • SANI GURGU – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.
  • UMARU DAN NIGERIA – Rafi, ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara.
  • NAGALA – Ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.