Shugabannin ƙasashen Turai sun fara gudanar da taron su a Budapest, inda suke fatar hada kansu domin tinkarar duk wata barazanar da ke iya tasowa daga shugabancin Donald Trump sakamakon nasarar zaɓen da ya yi.
A wa’adinsa na farko, shugaba Trump ya dinga takun saka da wasu shugabannin Turai musamman a ɓangaren kasuwanci da kuma biyan kuɗaɗen tafiyar da ƙungiyar kawancen tsaro ta NATO wanda wasu kasashe ke jan kafa a kai.
Shugabar gudanarwar ƙungiyar Ursula ɓon der Leyen ta bayyana cewar manufarsu itace haɗa kai domin tinkarar matsalolin da ke gaban su tare.
Shi kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan lokaci ne na su a Turai domin ɗaukar mataki mai ƙarfi. Macron ya yi tamabayar cewar, za su zuba ido ne domin karanta tarihin yaƙin da ɓladimir Putin ya kaddamar ko na zaɓen Amurka ko kuma zaɓin da mutane Chana suka yi? Maimakon tarihin da su zasu rubuta wajen jagorancin yankin.
Watanni kafin gudanar da zaɓen Amurka, shugabannin ƙasashen Turai suka fara tunanin yadda dangantakarsu za ta kasance da ƙasar idan tsohon shugaban ƙasa Donald Trump ya samu nasara, musamman abinda ya shafi tsaron yankin da kuma harkokin kasuwanci.
Shugaba Macron da Olaf Scholz na Jamus sun daɗe suna bayyana aniyar ganin ƙungiyar ƙasashen Turai ta tsaya da ƙafafuwarta maimakon dogaro da ƙasar ta Amurka, musamman a ƙarƙashin jagorancin Trump wanda ba shi da tabbas.
Shugaban ƙungiyar na karba karba Victor Oban na daga cikin na hannun damar Donald Trump da shugaban Rasha Vladimir Putin, kuma yana yawan samun takun saƙa da takwarorinsa da ke yankin.