
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar sojoji ta yi nasarar ceto ƴan mata guda 12 da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi awon-gaba da su a Gundumar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.
A makon da ya gabata ne aka yi garkuwa da su waɗanda galibinsu ƴan shekaru 15 zuwa 20 ne a yayin da suke tsaka da aiki a wata gona. Sun kuma samu ƴanci ne a jiya Asabar, 29 ga watan Nuwamba.
Hakan ya biyo bayan da dakarun tsaron ƙarƙashin atisayen Haɗin Kai suka ƙaddamar da aikin ceton sakamakon samun bayanai na sirri a yankin kudancin jihar.
A wani saƙo da Hedikwatar Rundunar ta fitar a Facebook a safiyar yau Lahadi, ta ce tuni aka garzaya da ƴan matan zuwa wani wajen sojoji inda ake da ba su kulawa, inda da zarar an kammala aiki akansu, za a damƙa su ga iyalansu.
Ga jaddawalin sunaye da shekarunsu: Fatima Shaibu (17), Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18), Saliha Muhammed (15), Sadiya Umaru (17), Amira Babel (15), Zara Adamu (17), Nana Shaibu (15), Zainab Musa (18), Zainab Muhammed (17), Jamila Saidu (15) da Hauwa Hamidu (17).
Rundunar ta kuma yaba wa ƙoƙarin dakarun bisa hoɓɓasa da suka yi a yayin jin aukuwar lamarin su da sauran masu ruwa da tsaki.
Kazalika, ta yi kira ga al’umma da su riƙa aiko da rahotonni na ababen da ke faruwa a yankunansu domin taimaka wa jami’an a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a shiyyar da ma arewacin Nijeriya baki ɗaya.
