Sojoji sun gudanar da musabaƙar Alƙur’ani a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Operation Hadin Kai ta sojin Nijeriya da ke yaki da Boko Haram ta gudanar da gasar karatun Al-Kur’ani ta matasa a yankin Monguna na Jihar Borno.

Muhammad-Nur Mustapha, wanda ya zama gwarzon gasar, ya samu karramawa da kyautar kujerar zuwa aikin Umrah.

Wanda ya zo na biyu kuma, Zaharadeen Yusuf ya samu kyautar kuɗi Naira 300,000 sai Mohammed Ali  da ya zo na uku da aka ba wa kyautar kuɗi Naira 200,000. Sauran wadanda suka samu karrmawa sun haxa da wanda ya fi iya ƙira’a da dai suransu.

Babban Limamin Monguno, Alhaji Liman Kaumi, ya jagoranci malamai wajen halartar ta musabaqar Al-Ƙur’ani da sojojin suka shirya, a yayin da Ajiyan Monguno, Alhaji Zanna Bulama, ya jagorinci sarakuna zuwa taron.

A jawabinsa na buɗe musabakar, mai masaukin baki kuma Kwamandan Runduna ta 111, Manjo-Janar A.E Abubakar, ya ce gasar za ta taimaka wajen samun nasara a yaqi da ta’addan ba tare da amfani da ƙarfin soji ba.

Ya bayyana cewa Babban Kwamandan rundunar, Manjo-Janar I.S Alkali, ya kirkiro ya kuma ɗauki nauyin gasar karatun Al-Kur’anin ne da nufin ganin al’umma sun samu ƙarin kusanci da Allah da kuma cusa wa mutanen yankin ƙaunar sojoji.

Manjo-Janar I.S. Ali, ya ce musabakar za ta qara ɗora matasa a turbar da za su fahimci addinin Musulunci yadda ya kamata da kuma wanzar da zaman lafiya.

Don haka ya buƙaci samun karin haɗin kai daga masu ruwa da tsaki domin tabbatuwar zaman a faɗin Jihar Borno.

Kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya bayyana cewa shirya musabaqar wata hanya ce ta ƙara kyautata alaka da ƙarfafa haɗin kan da sojoji ke samu daga al’ummar wajen yaƙi da ta’addanci.

A sakonsa ga taron, Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulumi, wanda Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Monguno, ya wakilta, ya jinjina wa sojojin bisa shirya musabaƙar da kuma nasarorin da suke samu a yaƙi da ta’addanci ba ta hanyar soji ba.

Ya kuma nuna godiyarsa bisa tabbacin da ya samu daga Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya wajen ci gaba da murƙushe ayyukan ta’addanci a faɗin jihar.