Sojoji sun kai samame gidan tsohon ministan Buhari kan hannu a juyin mulki, sun kama ɗan uwansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu dakarun tsaron Nijeriya a Abuja, sun mamaye gidan tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, bisa zargin sa hannu a yunƙurin juyin mulkin da ake bincike akansa ƙarƙashin Hukumar Leƙen Asirin Soji ta DIA.

A cewar jaridar SaharaReporters kamar yadda IntelRegion ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da atisayen ne a gidan Sylva da ke unguwar Maitama a birnin.

Majiyoyin sun ce, wata tawagar sojoji ne ta kai samamen sakamakon samun wani bayani na sirri da ke nuna tsohon ministan yana da hannu a lamarin bayan zargin sa da yin tattaunawar sirri da wasu daga cikin sojojin da aka tsare akan batun.

Haka kuma ana ganin Sylva ya tsere daga Nijeriya ne zuwa wata ƙasa domin neman mafaka, kamar yadda wani daga cikin majiyoyin ya shaida wa manema labarai.

Saidai duk da haka, jami’an sun yi nasarar kama ɗan uwan tsohon gwamnan, wanda ake kira da Paga. An kuma faɗaɗa atisayen zuwa gidansa na Bayelsa.

Wani jami’i da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce ana gudanar da ire-iren atisayen ne a yayin da aka samun bayanan sirri da suka danganta wasu ƴan siyasa da hannu a lamarin.

Ci-gaban na zuwa ne kwanaki kaɗan da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ofisoshin jagororin tsaro garambawul bayan zargin yunƙurin juyin mulkin a Nijeriya.

By Babaji