Sufeto Janar ya haramta wa abubuwan hawa amfani da gilashi mai duhu, shingayen bincike

Daga AISHA ASAS

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alƙali Baba, ya bada umarnin dakatar da amfani da gilashi mai duhu a motoci a faɗin Nijeriya.

A Litinin da ta gabata Baba ya ba da wannan umarni yayin wata ganawa da ya yi da manyan jami’an ‘yan sanda daga jihohin ƙasa.

Da alama dai ɗaukar matakin haramta wa motoci amfani da gilashi mai duhu na da nasaba da batun yaƙi da matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya.

Baya ga haka, Baba ya jaddada cewa haramun ne kafa shingayen bincike a kan hanyoyi a faɗin ƙasa, tare da gargaɗin cewa wajibi ne shugabannin kwamand-kwamand su tabbatar da an kiyaye wannan umarni kana a shiga yin sintiri a kan hanyoyi a madadin shingayen bincike.

Da ya taɓo batun masu aikata manya laifuka, IGP ya ce ‘yan sanda na tsare da wasunsu da suka haɗa mambobin IPOB da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji waɗanda sun amsa aikata wasu laifuka a baya-bayan nan.

Ya ce akwai buƙatar manyan jami’an su tabbatar da ɗa’ar aiki a tsakanin jami’an da ke ƙarƙashinsu.

Babban Sufeton ya bayyana wasu nasarori da rundunar ta samu cikin watanni biyun da suka gabata da suka haɗa da; kama sama da mutum 600 da ake zargi, ciki har da waɗanda ake zargin su ne suka kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai hari a watan Maris da ya gabata.

Wannan shi ne karon farko da IGP ya kira irin wannan taro tun bayan da aka naɗa shi muƙamin IGP.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*