
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS, ta shigar da ƙarar tuhumar aikata ta’addanci akan manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru da aka alaƙanta da Al-Ƙaida guda biyu a kotu bisa zargin su da hannu a munanan hare-hare a Nijeriya.
Mutanen sune Mahmud Usman da aka sani da Abu Bara’a Abbas/Mukhtar, wanda shi ne aka ayyana a matsayin Sarkin Ansaru, da kuma mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri, wanda aka sani da Malam Mamuda.
A kwanan nan jami’an tsaro suka yi nasarar kama su yayin gudanar da wasu atisaye a sassan ƙasar.
A cewar sashen bincike, daga cikin ababen da ake tuhumar su a kansu akwai, jagorancin ƙungiyar ta’addanci, ɗaukar nauyin ayyukanta, ɗaukar mayaƙa aiki a ƙarƙashinta da kitsa kai munanan hare-hare a faɗin Nijeriya.
Haka kuma ana zargin su da hannu a mummunan harin fasa magarƙamar Kuje a watan Yulin 2022, lamarin da ya yi sanadin tserewar sama da fursunoni guda 600 ciki har da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne da aka garƙame.
DSS ta kuma ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne makonni uku da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro NSA, Nuhu Ribaɗu ya sanar da kama su.
