Ta’addanci: Kotu ta yanke wa jagoran ISWAP da DSS ta gurfanar hukuncin ɗaurin shekara 20

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar ISWAP da Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi bisa zargin sa da ayyukan ta’addanci, wato Hussaini Ismaila, zai shafe tsawon shekaru 20 a kurkuku bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukunci.

Mai Shari’a, Emeka Nwite ya bayyana hukuncin a yayin shari’ar da ya gabatar a yau Talata bayan gano Ismaila, wanda ake kira da Mai Tangaran, yana da hannu dumu-dumu a laifuka huɗu masu alaƙa da ta’addanci da DSS ta gabatar akansa.

An samu mai laifin da shirya hare-haren 2012 a hedikwatar ƴan sanda ta Bompai a Jihar Kano, sansanin ƴan sandan Mobile, harin Pharm Center, harin ofishin ƴan sanda na Unuguwa Uku da sauransu waɗanda dukkaninsu sun raunata mutane da dama.

Jim-kaɗan bayan kama shi a ranar 31 ga watan Agustan 2017 a Ƙauyen Tsamiya Babba na Ƙaramar Hukumar Gezawa, aka gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume guda huɗu waɗanda aka kafa hujja da dokokin haramta ta’addanci na 2013 a kansu.

An yi ta samun jinkiri a shari’ar a sakamakon bincike da ƙoƙarin tantance hujjoji a lokuta daban-daban, inda daga bisani DSS ta gabatar da jami’anta biyu a matsayin shaidu ga wasu daga cikin hare-haren.

Da fari, ɗan ta’addan ya musanta hannu a laifukan da ake tuhumar sa a kansu, wanda ya sauya zuwa amsa aikata su a lokacin da shaida na biyar ya tabbatar da tuhume-tuhumen.

By Babaji