‎Gidauniyar Musa Adamu Gwagware Network za ta raba magungunan cutar fata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban gidauniyar Kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce tuni gidauniyar ta sayi magungunan na miliyoyin Naira domin rabawa kyauta ga masu wannan cuta a yankin Funtua.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa har wala yau gidauniyar ta baza ƙwararrun malaman kiwon lafiya na fannin cutar fatar zuwa ƙauyukan da ke yankin domin gano da tantance masu ɗauke da cutar kafin basu maganin.

Ya ce cutar da ya haɗa da kyasfi da saurar cutukan da suka shafi fatan mutum “yara mabarata suka fi ɗaukar cutar saboda rashin tsabtace kansu da makwancin su.

Shugaban gidauniyar wanda tsohon ma’aikacin kiwon lafiya ne ya bayyana ƙudirin su na cigaba da samar da tallafin magunguna da kuɗi ga marasa lafiya a yankin Funtua da na faɗin jihar Katsina baki ɗaya.

Kwamred Suleiman ya kuma yaba da yadda gwamna Dikko Raɗɗa ke ba harkar kiwon lafiya mahimmancin ta hanyar maida ƙananan asibitoci zuwa manya tare da samar masu da na’urorin kiwon lafiya na zamani a faɗin jihar.

Haka ma ya ƙara yabawa gwamnan kan yadda harkokin lafiya ya zama na uku a wajen kaso na kasafin kuɗi na 2026.

“Aiko kaga ta zama wajibi mu zo mu bada tamu gudunmawa iya ƙarfinmu wajen kyautata harkokin kiwon lafiya a jihar Katsina,” inji Kwamred Suleiman.

By ukarofi