Shugaban ƙaramar hukumar Funtua ya ƙaddamar da masu bashi shawara guda 50

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Da yake ƙaddamar da mashawartan a ɗakin taro na ƙaramar hukumar, shugaban Alhaji Abdulmutallab Suleiman Goya ya shawarce su da su yi amfani da basirar su wajan bada ta su gudunmawar ga cigaban ƙaramar hukumar gaba.

Ya bayyana cewa sai da aka ba duk mazaɓu a ƙaramar hukumar damar wajen zaƙulo waɗanda za su bada shawarar da suka haɗa da matasa,masu buƙata ta musamman,mata ,yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar.

Hon Abdulmutallab ya sanar da cewa wannan masu bada shawara kashi na farko ne a yayin da kashi na biyu suma za su sami irin wannan muƙami a ƙarshen wata mai zuwa.

Ya miƙa godiyar sa ga gwamna Dikko Raɗɗa bisa zuba manyan ayyuka a ƙaramar hukumar ta Funtua.

Ayyukan kuwa ya ce sun haɗa da gina tagwayen hanyoyi da gyaran wasu a cikin garin Funtua,gina katafaran cibiyar koyon sana’o’i, gina babban ofishin yan sandan kwantar da tarzoma da kuma ƙaramin filin jirgin sama na kwasan kaya a Makwalla.

A jawabinsa na maraba, sakataren ƙaramar hukumar Hassan Musa Anda ya bayyana cewa kafin naɗa waɗannan masu bada shawara sai da suka tuntuɓi masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar.

Ya shawarci ma su bada shawarar da su yi amfani da ɗimbin basirar su wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar.

Sauran waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu sun haɗa da Sarkin Maska Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo da Dattijo Usman Musa Alaliya.

By ukarofi