Shigar-burtu ga Hausawa

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Karya fure ta ke ba ta ‘ya’ya. ‘Yan kwangilar rusa Arewa sun yi tsammanin za su iya basaja da yin shigar-burtu wai su Hausawa ne sai kawai a kyale su, ko ma a rika rarrashinsu don kar su tada hankali ga takarkarewa da su ka yi sai sun kunna fitinar ƙabilanci. Fasa mu su taya da fito da su a matsayin makiya Hausawa da addinin Hausawa ya sa su ka koma zunduma ashar ta uwa ta uba. Yo in ba ɗan banza bakwai na zamanin yau ba, waye zai zayyana hoton gwagwarmayar Hausawa da wani baubawan burmi ya na busa! Hoton Bahaushe kenan fa a idon wadannan ma’abota annamimanci inda su ka ɗauka ƙida da waka a ƙofar gidan Sarki wata daraja ce. Irin waɗannan alamu na daga abubuwan da su ka sa na shiga kokonton kai waɗannan ba Hausawa ba ne. Mu na ci gaba da rubutu sai su ka fara fitowa da hotonsu daga martanin da su ke yi kamar “Ni ƙabilanci na ke yi don ƙabila jini ce, addini zaɓi ne!” Ba Bahaushe mai sallah da zai faɗi haka. Can wani sai ya rubuta “gara min Bamaguje da Limami Bafulatani” Sam ba Bahaushe Musulmi da zai faɗi haka. Can sai mu ka fara fahimtar ashe hatta wasu daga cikin waɗanda su ke kama da Musulmi har da sa alamun Musulunci ba Musulmi ba ne shuka su a ka yi don su rura wutar fitinar ƙabilanci a tsakanin Musulmi a yi ta ɗauki ba daɗi. Wallahi su na gogawa mabiya addinin Kirista kashin kaji don haƙiƙa mun san yadda su Pastor Yohanna YD Buru da Pastor Aminci Abu hard a Moɓel Wuye ke kira kan zaman salama. Ya zama wajibi duk ɗan Arewa ya wanzar da alaƙar kirki ta zaman tare tsakanin dukkan mazauna yanki mabiya kowane addini da mazauna kowane gari.

A yanda na ke gani wadannan dai masu karyar Hausa zalla ɗin nan ba za su iya haddasa yaƙin da su ke buri ba don cimmawa iyayen gidansu buri na tsawon shekaru tun zamanin mulkin mallaka. Rashin fahimtar ruhin addini ya sa ‘yan kwangilar makancewa da tunanin za su iya yaudarar jama’a. Ko a shafukan kyauta na soshiyal midiya da su ke fesa gubar zindikancinsu, an samu wasu matasa da ke daidai da su. Duk da nacin da su ke da shi na martani ba dare ba rana don cin kuɗin kwangila, amma ƙalubalen da su ke samu daga Hausawan gaskiya na zama mu su ƙadangaren bakin tulu. Da zarar sun ga karya ta kare sai su shiga sharri su na danganta Hausa/Fulani da marawa ta’addanci baya. Na yi bayani a baya cewa da waɗannan ‘yan ta’addan soshiyal midiya Hausawan bogi da ɓarayin daji duk tafiyarsu daya sammakal. Kamar yanda miyagu da a ka sha kamawa daga Arewa ta tsakiya masu sayarwa ‘yan ta’addan daji makamai ba sa ƙaunar ƙarewar fitinar nan; haka ma waɗannan ‘yan Yausawa Zalla su ke. Ai in an kwantar da fitinar ɓarayin daji ba za su samu damar cigaba da shirga karya da alaƙanta Mujaddadi Shehu ɗanfodiyo da waɗannan miyagun ba. Na saurari bayanan da Bulama Bukarti ya gabatar kan yanda a ka ƙulla makircin. Abun takaicin yanda hakan ke fitowa daga ƙasashen yammacin duniya da ya dace su rika taimakawa al’ummar Afurka da har yau ba su gama farfaɗowa daga mulkin mallaka ba.

Ina amfani da wannan dama wajen kira ga ƙungiyar Kiristocin Nijeriya ta CAN da ta tsawatawa wasu daga masu wa’azi da sunan Kirista da ma ‘yan shigar burtun nan su canja sana’a. Gaskiyar magana matuƙar wannan wutar da su ke kunnawa ta tashi ko da wasunsu na gantali a ƙetare, to ai akwai danginsu. Fitina kan shafi hatta wanda ke barci a cikin ɗakinsa. Mun ga yadda Isra’ila ta rika ruwan boma-bomai kan Falasɗinawa a Gaza inda wasu su na barci ma a ka yi mu su kisan gilla.

Kazalika ina kira ga dukkan masallatai a Arewa a dage da addu’o’in ALKUNUT don neman taimakon Allah ya yi ma na maganin ‘yan ta’addan soshiyal midiya masu kunna wutar ƙabilanci da ‘yan uwansu ‘yan ta’addan daji. Hakanan Allah ya kare Arewa da tarayyar Nijeriya daga duk wata barazana daga ƙetare. Na tabbata Allah mai jin roƙon bayinsa ne. In Allah ya yarda a dan kankanin lokaci za a ga taimakon Allah, miyagun nan duk za a daina jin duriyarsu matuƙar su ka ƙi tuba.

Na yi ƙalubale na cikon 7 kan masu karyar gwagwarmaya su bayyana kan su a san su. Duk wanda ya cigaba da kasancewa a ɓoye “locked profile” kamar kartagi uban ‘yan kwangila Ouba Ali Mohaman na Kamaru, za mu yanke matsaya cewa makiri ne kuma matsoraci don haka hukuma ta gaggauta cafke shi ya fuskanci tuhumar cin amanar ƙasa. Ba ƙasar da zata ci gaba duk karfin arzikin ta na ma’adinai sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa. Lamarin zaman lafiya ya haɗa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma ƙabilu daban-daban a irin kasa kamar Nijeriya.

Maimakon wasu, su dan yi ta maza su bayyana bayan buƙatar da mu ka yi ta tsawon mako daya; sai ‘yan iƙirarin ƙaryar Hausa Zalla su ka kara lulluɓe kan su da bargon makirci don kwangilar da makiya Arewa su ka ba su, ta kasa samun nasara in ka ɗebe maganganun shiririta a yanar gizo. Aƙalla an yi tsammanin za a ga masu surfa ta miyagun kalamai sun fito da hotuansu da sunayensu na gaskiya su George, Irmiya, Angulu, Annabi Zamani da sauransu, sai su ka turo wani ya yi yekuwa cewa su dodannin ɓoye ne wai a na bin su ta akwatin ajiye sako a na caccakar su. Haba wa zai bi matsoraci har cikin gida ya tanka ma sa. Marigayi Mahdi mai dogon zamani Dokta Mamman Shata a waƙar Ummaru Dan-Dan Duna ya na mai cewa “Ummaru ne ga shi nan a sarari sai mai waƙa su ke ha harara…Dau gora tittike abunka, kisan biri ba sai da I igwa ba” Sauran bayani a saurari waƙar Dokta za a gane ba bukatar damuwa da matsoraci. Na ma sha fada a baya cewa Wallahi mutanen nan ‘yan basaja ba su kai a tanka mu su ba, amma la’akari da salon shigar-burtu da su ke yi ya sa ya ke da muhimmanci mu riƙa haska su don matasanmu su ankare kar su faɗa tarkon su.

A fili kamar hasken rana miyagun nan sun zaɓi su zama Hausawa ne don fahimtar yadda addinin Musulunci ya zama na Hausawa. Hasalima in ka shiga yankunan da ba na Hausawa ba da shiga irin ta Hausawa ka zama Musulmi ko da kuwa kai Kirista ne daga Kagoro ko Samarun Kataf. Mutanen sun dage sai sun ɓata dangantakar da Musulmi da mabiya addinin kirista ke da ita tun zamanin Firamiya Sir Ahmadu Bello. Hanya mafi sauki ga mutanen nan su huce haushin su ga Hausawa da ke kyamar bin hanyar matsafa shi ne su nuna su Hausawa ne har ma kare muradun Hausawa su ke yi. Sun ma nada kan su mukamai da ba sa hannun ko daya daga cibiyoyin Hausa na jami’o’inmu a Arewa. In gaskiya ne ta yaya mai kare muradin Hausawa zai boye kan sa ya ƙirƙiro sunan bagaye ya ce Hausawa ya ke karewa? Mene ne laifin mai kare Hausa da Hausawa a Arewa? Don haka tabbas duk wanda ya yi shigar burtu munafuki ne dan kwangila maƙiyin Hausawa mai son tada fitinar ƙabilanci don wargaza ƙarfin Arewa a addinance da a siyasance. 

KAMMALAWA

A kwanakin baya na ga makiran nan na yaba wa Audu Bulama Bukarti da cewa jajirtacce ne wajen nazari da marawa gaskiya baya. Kazalika sun ma yaba wa yankinsa na Arewa maso gabar da nuna ai al’ummar yankin sun gwale ‘ya’yansu da su ka shiga Boko Haram su ka fito da su a ka murƙushe su. A lokaci guda su ka zargi wasu a Arewa maso yamma da ɓoye ɓarayin daji da hakan shirga karya ne don dan ta’adda ai ba ruwansa da ƙabilarka ko ma addininka. Fallasa asirin wani taro a Burtaniya na ƙullawa Arewa maƙarƙashiya da Bukarti ya yi ya sa yanzu kuma ya zama abun caccaka daga miyagun nan don an fallasa asirin sashen masu daukar nauyin kamfen ɗin su na kunna wutar fitinar ƙabilanci. Aikin kawai wai an yakushi kakkausa, wannan ba zai hana kara tona asirin miyagu maƙiya Hausawa da Arewa ba, masu mugun nufi tun zamanin mulkin mallaka. Dillalan sharhi irin su Ouba Ali Mohaman na Kamaru ma sun koma ƙarƙashin kasa da makircin na su don ruhin addini na Arewa ba zai ba su damar cigaba da cashewa da rawar gaban hantsi ba. Irin su fito ma na su kwashi kashinsu a hannu ta hanyar hujjoji da ba za su kankaru ba.

Jama’a zan ɗiga aya a nan da ƙara nanata cewa lallai a cigaba da ƙalubalantar ‘yan kwangila su fito fili a san da wa a ke cacar baki don Bahaushe sam ba ya buƙatar buya a ramin kura don zangar zai bayyana ra’ayi kuma ko ma wane irin ra’ayi ne a dai nan ƙasar Arewa.

By ukarofi