Tallafin Tinubu ya rage wahalar marasa lafiya masu ciwon ƙoda na asibitin Aminu Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsawon shekaru sashen wanke ƙoda na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya kasance cike da damuwa da takaicin marasa lafiya da suke fama da cutar ƙoda, saboda tsadar jinyar. A baya, kowanne aikin zaman wanke ƙoda yana kaiwa tsakanin Naira 50,000 zuwa Naira 60,000, abin da ya sa da yawa suka daina zuwa asibiti — abin da yakan kai ga mutuwa.

A yau kuwa, wannan yanayi ya sauya gaba ɗaya. Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da wani gagarumin tallafi wanda ya rage kuɗin zaman wanke ƙoda da har kaso 80 cikin 100, daga N50,000 zuwa N12,000 kacal a kowane zama. Wannan tallafi, wanda ya shafi manyan asibitoci 11 na tarayya, ya riga ya fara sauya halin da ake ciki a AKTH — inda ake samun ƙaruwa sosai a yawan marasa lafiya da ake jinyar su, tare da ceton rayuka da dama.

“A da, yawancin marasa lafiya ba sa iya zuwa akai-akai saboda tsadar jinyar,” inji Tijjani Rahim, Mataimakin Daraktan Sashen Kula da Ma’aikatan Jinya kuma Shugaban Sashen Wanke ƙoda na AKTH. “Amma tun da aka kawo tallafin, yanzu muna karɓar marasa lafiya kimanin 22 zuwa 25 a kullum. Bambancin ya bayyana sosai.”

Rahim ya bayyana cewa AKTH na daga cikin asibitocin farko da suka ji tasirin wannan tallafi kai tsaye, inda Gwamnatin Tarayya ta samar da kayan amfani na musamman don gudanar da zaman wanke koda 1,000 kyauta ko a rangwame. Sakamakon haka, marasa lafiya da suka daina zuwa sun koma asibiti da sabuwar fata.

Malam Sani Musa, wanda ya daɗe yana fama da cutar ƙoda, ya bayyana wannan tallafi a matsayin “mu’ujiza.”

“A baya, ina biyan tsakanin N54,000 zuwa N60,000 a kowane zama,” inji shi da farin ciki. “Daga baya ya sauka zuwa N20,000, yanzu kuma N12,000. Wannan ya bani damar sake rayuwa.”

Wani mara lafiya, Mamuda Aliyu, ya ce wannan sauƙin ya ba shi damar ci gaba da jinyar sa ba tare da yankewa ba.

“A lokacin da yake N60,000, na kusa daina zuwa. Amma N12,000 yana yiwuwa. Ina roƙon gwamnati ta ci gaba da wannan shiri,” inji shi.

Haka ma Hafiza Isa ta tuna wahalar da ta sha a baya lokacin da kuɗin zaman yake tsakanin N60,000 da N45,000.

“Yanzu ina iya tsara rayuwata yadda ya dace. Wannan tallafi ya sauke nauyi mai girma daga kafaɗata,” ta ce.

A cewar ma’aikatan asibitin, wannan tsari na gwamnati ba wai kawai ya rage wa marasa lafiya ƙunci ba ne, har ma ya farfaɗo da kwarin gwiwar ma’aikata da dangin marasa lafiya da suka sha wahala saboda tsadar jinya.

A ƙarshe, marasa lafiya da dama sun gode wa Gwamnatin Tarayya bisa wannan shiri na taimako, suna roƙon a faɗaɗa tsarin zuwa sauran asibitoci da kuma yiwuwar kyautata shi har zuwa matakin kyauta ga talakawa masu tsananin buƙata.

“Gwamnati ta nuna kulawa ga rayuwar talaka. Muna fatan wannan tallafi zai ɗore,” inji wani daga cikin marasa lafiya da ke AKTH.

By ukarofi