Ku fara ceto masu raunin harbi kafin rahoton ’yan sanda – Gargaɗin ƙungiyar likitoci ga asibitoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

ƙungiyar Likitocin Masu Neman ƙwarewa ta ƙasa (NARD) tare da Majalisar Jinya da Ungozoma ta Nijeriya (NMCN) sun sake jaddada umarnin cewa duk asibitoci su riƙa karɓar masu rauni sakamakon harbin bindiga nan take — ba tare da neman rahoton ’yan sanda ba.

Sun yi wannan kira ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, bayan yawaitar ƙorafe-ƙorafen da ake samu kan wasu asibitoci da ke ƙin karɓar irin waɗannan marasa lafiya.

Dokar kula da mutanen da aka ji wa rauni ta hanyar harbin bindiga, wacce aka amince da ita a shekarar 2017, ta wajabta a yi wa duk wanda ya ji rauni irin haka magani nan take, ko a asibitin gwamnati ko na masu zaman kansu, ba tare da wata takardar ‘yan sanda ba.

Sashe na 7 na dokar ya tanadi hukunci ga duk wanda sakaci ko ƙin taimakonsa ya jawo mutuwar wanda aka ji wa rauni — inda zai fuskanci ɗauri na shekaru biyar, tara ta N500,000 ko duka biyun.

A cikin wata sanarwa da hukumar ‘yan sanda ta fitar a ranar 25 ga Oktoba, 2023, an umurci jami’an ta su tabbatar da bin wannan doka kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba.

Shugaban ƙungiyar NARD na ƙasa, Dokta Mohammad Suleiman, ya bayyana ƙin karɓar masu rauni a irin waɗannan lokuta a matsayin “abin da ba za a lamunta ba”, yana mai cewa aikin likita shi ne ceton rai, ba yin shari’a ba.

Ya ce, akwai yiwuwar wasu likitoci ba su da cikakken ilimi game da dokar, amma ƙungiyar NARD na ci gaba da wayar musu da kai ta shirin horaswa kan al’amuran doka da na aikin lafiya.

A cewarsa: “A inda nake aiki a Katsina, muna fara magani ne kai tsaye. ‘Yan sanda ne ke bin sauran matakan. Aikinmu shi ne ceton rai.”

Ya ƙara da cewa, duk asibitin da ya ƙi karɓar mai rauni yana aikata laifi kuma hakan ya saɓa wa ƙa’idojin aikin lafiya.

Suleiman ya nemi a kai likitocin da suka aikata hakan gaban hukumar kula da likitoci (MDCN) domin hukunta su.

Shi ma Sakatare Janar na Majalisar Jinya da Ungozoma (NMCN), Ndagi Alhassan, ya ce wasu ma’aikata na bin wasu ƙa’idoji na cikin gida da ke sabawa umarnin Gwamnatin Tarayya kan kula da gaggawa.

By ukarofi